Shugaba Tinubu Zai Tafi Ziyarar Aiki a Gobe Asabar Zuwa Kasashe Uku

Daga Bashir Gasau.   A gobe Asabar, 2 ga watan Mayun shekarar 2026, Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai tafi ziyarar aiki zuwa kasashe Uku.   Mashawarcin Shugaban kasar kan yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce kasashen da Tinubu zai […] The post Shugaba Tinubu Zai Tafi Ziyarar Aiki a Gobe Asabar Zuwa Kasashe Uku appeared first on GTR .

Shugaba Tinubu Zai Tafi Ziyarar Aiki a Gobe Asabar Zuwa Kasashe Uku

Daga Bashir Gasau.

 

A gobe Asabar, 2 ga watan Mayun shekarar 2026, Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai tafi ziyarar aiki zuwa kasashe Uku.

 

Mashawarcin Shugaban kasar kan yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce kasashen da Tinubu zai je sun hadar da Kenya, Rwanda da kuma Faransa.

 

Dole APC ta Hana Tinubu Takara Matuƙar Tana so Taci Zaɓen Shugaban Ƙasa – Dakta Sunusi Balarabe na Jam’iyyar APC

 

Da farko Shugaban zai fara da kasar Faransa, daga nan kuma zai wuce birnin Nairobi na ƙasar Kenya, domin halartar taron Afirka da Faransa wanda za a fara a mako mai zuwa.

 

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, da Shugaban Kenya, William Ruto, ne za su jagoranci taron wanda za a yi a ranakun 12 da 13 ga watan Mayu, inda zai mayar da hankali kan sauyin makamashi, masana’antu masu kare muhalli, sauyin fasahar zamani, sake fasalin tsarin kuɗaɗen duniya, da matakan yaƙi da sauyin yanayi.

 

Rayuwa Sai da Magani (2): Magani a Cikin Abincinmu na Yau da Kullum

 

Bayan kammala taron Kenya, Shugaba Tinubu zai tafi Kigalin kasar Rwanda, domin halartar taron shekara-shekara na Africa CEO Forum, wanda za a gudanar daga ranar 14 zuwa 15 ga watan Mayu, inda aka shirya taron tare da haɗin gwiwar International Finance Corporation (IFC), kuma zai haɗa manyan shugabanni sama da 2,000 domin tattauna hanyoyin gina masana’antu masu juriya da gasa.

 

A yayin tarukan biyu, Shugaba Tinubu zai gabatar da jawabai kan sauye-sauyen da gwamnatinsa ke yi, domin mayar da Najeriya wuri mafi dacewa ga zuba jari da ci-gaba, baya ga ganawar da zai yi da manyan shugabannin fannin kasuwanci na duniya da na Afrika.

 

Tawagar Shugaban kasar za ta ƙunshi Ministoci, da manyan masu ba shi shawara, inda ake sa ran zai dawo gida Najeriya bayan kammala taron kasar Rwanda.

 

Nasarar ADC a Kotun Ƙoli Tana Ƙasa Tana Dabo – Barista Abba Hikima

The post Shugaba Tinubu Zai Tafi Ziyarar Aiki a Gobe Asabar Zuwa Kasashe Uku appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow