Satar Mutane a Oriire: Majalisar Dattawan Najeriya ta Ware Naira Milyan 50 Don Tallafa wa Iyalan Wadanda Lamarin ya Shafa

Daga Bashir Gasau.   Majalisar Dattawan Najeriya, ta sanar da ware Naira Milyan 50 domin tallafa wa iyalan mutanen da suka gamu da Iftila’i a batun garkuwa da mutanen da ya faru a Ƙaramar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo.   Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya sanar da hakan a yayin zaman Majalisar […] The post Satar Mutane a Oriire: Majalisar Dattawan Najeriya ta Ware Naira Milyan 50 Don Tallafa wa Iyalan Wadanda Lamarin ya Shafa appeared first on GTR .

Satar Mutane a Oriire: Majalisar Dattawan Najeriya ta Ware Naira Milyan 50 Don Tallafa wa Iyalan Wadanda Lamarin ya Shafa












Daga Bashir Gasau.

 

Majalisar Dattawan Najeriya, ta sanar da ware Naira Milyan 50 domin tallafa wa iyalan mutanen da suka gamu da Iftila’i a batun garkuwa da mutanen da ya faru a Ƙaramar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo.

 

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya sanar da hakan a yayin zaman Majalisar na jiya Laraba, inda ya ce tallafin na daga cikin matakan da majalisar ke ɗauka domin rage musu raɗaɗin wannan mummunan lamari.

 

Chadi ta Sahalewar Al’ummar Nahiyar Afirka Izinin Shiga Kasar ba Tare da Visa ba

 

A cewar Akpabio, “An ware Naira Milyan 10 ga kowanne daga cikin iyalan jami’an tsaro ukun da suka rasu a yayin aikin ceto waɗanda aka sace. Haka kuma, iyalan malamai biyu da aka kashe za su karɓi Naira Milyan 10 kowannensu”.

 

Haka kuma Majalisar ta bayyana wannan tallafi a matsayin wani ɓangare na martanin da take bayarwa kan lamarin, tare da yin kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi da haɗin guiwa domin ceto sauran mutanen da har yanzu ke hannun masu garkuwa da mutane a sassa daban-daban na Najeriya.

 

Hisba ta Haramta Sana’ar Tura Fina-finai ta Wayar Salula (Downloading) a Faɗin Jihar Kano

 

Da yake gabatar da batun bisa ƙa’ida a zauren majalisar, Sanata me wakiltar Bauchi ta tsakiya, Abdul Ningi, ya buƙaci Majalisar ta tabbatar da cewa dukkan mutanen da hare-haren baya-bayan nan suka shafa sun amfana da diyya ba tare da nuna bambanci ba.

 

A ƙarshe yayi gargaɗin cewa bai kamata a nuna wariya wajen biyan diyya ga waɗanda irin waɗannan hare-hare suka shafa ba.

 

El-Rufai ya Nemi Afuwar Kotu Bayan ya Janye Wasu Bukatu Uku

The post Satar Mutane a Oriire: Majalisar Dattawan Najeriya ta Ware Naira Milyan 50 Don Tallafa wa Iyalan Wadanda Lamarin ya Shafa appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow