Sarkin Musulmin Najeriya ya Aiyana Gobe Litinin a Matsayin Ranar 1 ga Watan Zulhijja na Shekarar 1447

Daga Bashir Gasau.   Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na Uku, ta sanar da ganin jinjirin watan Zulhijja na Shekarar 1447, bayan hijirar Annabi Muhammad (S A W).   Shugaban kwamitin kula da harkokin addinin Musulunci, Farfesa Sambo Wali Junaidu (Wazirin Sokoto), ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa […] The post Sarkin Musulmin Najeriya ya Aiyana Gobe Litinin a Matsayin Ranar 1 ga Watan Zulhijja na Shekarar 1447 appeared first on GTR .

Sarkin Musulmin Najeriya ya Aiyana Gobe Litinin a Matsayin Ranar 1 ga Watan Zulhijja na Shekarar 1447

Daga Bashir Gasau.

 

Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na Uku, ta sanar da ganin jinjirin watan Zulhijja na Shekarar 1447, bayan hijirar Annabi Muhammad (S A W).

 

Shugaban kwamitin kula da harkokin addinin Musulunci, Farfesa Sambo Wali Junaidu (Wazirin Sokoto), ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Yau Lahadi, inda ya tabbatar da ganin jinjirin watan Zulhijja a yammacin yau.

 

Najeriya Da Jamus Sun Ƙulla Yarjejeniyar Zuba Jarin Dala Milyan 428

 

A cewar sanarwar Wazirin Sokoto, “Sarkin Musulmin kuma Shugaban Majalisar Ƙolin Shari’a ta Ƙasa (NSCIA), ya aiyana gobe Litinin, 18 ga watan Mayun shekarar 2026 a matsayin ranar 1 ga Zulhijja na Shekarar 1447”.

 

Sarkin Musulmin Najeriya ya Aiyana Gobe Litinin a Matsayin Ranar 1 ga Watan Zulhijja na Shekarar 1447

 

Watan Zulhijja dai shine na ƙarshe a Kalandar Musulunci me watanni 12, kuma a cikinsa Al’ummar Musulmin Duniya ke haduwa a ƙasar Saudiyya domin gudanar da ibadar aikin Hajji, wadda ta kasance daya daga cikin rukunan Musulunci guda Biyar.

 

Kuma dai tun a yammacin yau din itama kasar Saudiyya ta sanar da ganin jinjirin watan Zulhijja, harma ta aiyana ranar Talata, 26 ga watan Mayu a matsayin ranar “Arfah”, a inda Laraba, 27 ga watan Mayun ta kasance ranar Idin Babbar Sallah (Eid al-Adha).

 

An ga Watan Babbar Sallah (Zulhijja) a Ƙasar Saudiyya

The post Sarkin Musulmin Najeriya ya Aiyana Gobe Litinin a Matsayin Ranar 1 ga Watan Zulhijja na Shekarar 1447 appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow