NOA ta Fara Gangamin Wayar da Kan Matasan Jihar Bauchi Domin Inganta Tsaro

Daga Mu’azu Hardawa Bauchi.   Mataimakin Daraktan hukumar wayar da kan jama’a ta Kasa (NOA) reshen jihar Bauchi, Alhaji Adamu Garba Sarkin Yara, ya ce hukumarsu ta fara gangamin wayar da kan matasa don samun ingantaccen tsaro da zaman lafiya a jihar.   Alhaji Adamu Sarkin Yara, ya baiyana hakan a lokacin da ya kira […] The post NOA ta Fara Gangamin Wayar da Kan Matasan Jihar Bauchi Domin Inganta Tsaro appeared first on GTR .

NOA ta Fara Gangamin Wayar da Kan Matasan Jihar Bauchi Domin Inganta Tsaro

Daga Mu’azu Hardawa Bauchi.

 

Mataimakin Daraktan hukumar wayar da kan jama’a ta Kasa (NOA) reshen jihar Bauchi, Alhaji Adamu Garba Sarkin Yara, ya ce hukumarsu ta fara gangamin wayar da kan matasa don samun ingantaccen tsaro da zaman lafiya a jihar.

 

Alhaji Adamu Sarkin Yara, ya baiyana hakan a lokacin da ya kira taron manema labarai a ofishinsa da ke Bauchi, inda ya ce sun kaddamar da gangamin ne a dakin taro na gidan gwamnatin jihar Bauchi.

 

Gwamnatin Bauchi ta Kaddamar da Jami’an Sintiri 2100 Don Inganta Tsaron Dazuka da Yankunan Karkara

 

A cewarsa, “Mun gaiyaci ƙungiyoyin matasa daga kananan hukumomi 20 na jihar Bauchi, da kuma wakilan dukkan Jami’an tsaro da sarakunan gargajiya musamman na yankunan da ake fuskantar barazanar tsaro, don wayar musu da kai wanda kuma Gangamin zai ci gaba tun daga fadar jiha zuwa yankunan kananan hukumomi 20 na jihar nan”.

 

Ya kara da cewa matasa suna da rawar takawa a fannin samar da zaman lafiya don duk wata matsalar da ke tasowa idan suka bayar da hadin Kai za a sami nasarar daƙile ta cikin sauri kuma a saukake.

 

‘Yan Sandan Bauchi Sun Ceto Yaran da Aka Sato Daga Jihar Taraba Aka Boye a Jihar

 

Adon haka ya bukaci kowa ya zamo jakadan gwamnati wajen taimakawa don a samun ingantaccen tsaro a jiha da Kasa baki daya, tunda sai an hada kai za a gudu tare kuma a tsira tare.

 

A karshe ya ce sun gaiyaci mutane musamman daga ƙaramar hukumar Alkaleri kamar Sarkin Duguri da Hakimai da Dagatai da masu Unguwanni daga yankunan da Yan bindiga suka tarwatsa kamar su Mansur da Digare da kuma Gwana.

 

Gwamnatin Kano ta Dakatar da Bude Film House na Sultan Dake Unguwar Dorayi

The post NOA ta Fara Gangamin Wayar da Kan Matasan Jihar Bauchi Domin Inganta Tsaro appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow