NASSI ta Shirya Gagarumin Taro Don Bunkasa Kasuwanci a Jihar Kano

Daga Bashir Gasau.   Ƙungiyar Masu Ƙanana da Matsaƙaitan Masana’antu ta Ƙasa, wato Nigerian Association of Small Scale Industrialist (NASSI), reshen Jihar Kano, ta shirya wani gagarumin taron masu ruwa da tsaki a sha’anin kasuwanci a jihar.   Shugaban ƙungiyar na jihar Kano, Kwamared Aminu Ibrahim Kurawa (Dan Masanin Kabo), ne ya baiyana hakan a […] The post NASSI ta Shirya Gagarumin Taro Don Bunkasa Kasuwanci a Jihar Kano appeared first on GTR .

NASSI ta Shirya Gagarumin Taro Don Bunkasa Kasuwanci a Jihar Kano












Daga Bashir Gasau.

 

Ƙungiyar Masu Ƙanana da Matsaƙaitan Masana’antu ta Ƙasa, wato Nigerian Association of Small Scale Industrialist (NASSI), reshen Jihar Kano, ta shirya wani gagarumin taron masu ruwa da tsaki a sha’anin kasuwanci a jihar.

 

Shugaban ƙungiyar na jihar Kano, Kwamared Aminu Ibrahim Kurawa (Dan Masanin Kabo), ne ya baiyana hakan a yayin zantawar sa da GTR Hausa, inda ya ce sun shirya taron ne da hadin guiwar Gwamnatin Jihar da kuma Bankin Stanbic IBTC.

 

Atiku, Obi da Sauran ’Yan Takarar Shugabancin Najeriya ba su kai Tinubu Cancanta ba – NNPP

 

Bangarorin da aka gaiyato domin Bajakolin fasahohin bunƙasa kasuwanci, sun kunshi hukumomin Gwamnati a matakin tarayya da jiha kamar NAFDAC, Smeden BOA, BOI, AKK, SON, KIRS da dai sauransu.

 

A cewar Kurawa, “Dalilin shirya wannan taro shine domin haduwa fuska da fuska da wadannan bangarori don mu tattauna akan matsalolin da ke damun kasuwancin masu Kanana da Matsakaitan Masana’antu domin a magance su, harma da damarmakin da ake dasu domin amfanin jihar Kano”.

 

Shugaban Nijar ya Sauke Babban Hafsan Sojin Ƙasar

 

Taron dai zai gudana ne a ranar Asabar, 19 ga watan Satumbar shekarar 2026, a dakin taro ne Coronation Hall da ke gidan Gwamnatin Jihar Kano.

 

A ƙarshe Kungiyar ta yi fatan dukkan mahalarta taron za su bada cikakken hadin kai da goyon baya domin samun nasarar taron yadda ya kamata.

 

Sarkin Musulmin Najeriya ya Aiyana Gobe Lahadi a Matsayin Ranar Daya ga Watan Rabi’ussani na Shekarar 1448AH

The post NASSI ta Shirya Gagarumin Taro Don Bunkasa Kasuwanci a Jihar Kano appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow