Najeriya da Majalisar Dinkin Duniya za su Kara Hada Kai Don Kare Hakkin Dan Adam Da Tallafawa Wadanda Rikice-rikice ya Shafa

Daga Kallamu Galadima Dambo.   Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa (Mai Ritaya), ya sake jaddada kudurin gwamnatin Najeriya na ci-gaba da bin dokokin jin-ƙai na ƙasa da ƙasa, tare da mutunta haƙƙin ɗan Adam a dukkan aiyukan rundunonin tsaro.   Ministan ya bayyana hakan ne a Shelkwatar Ma’aikatar Tsaro da ke Abuja, yayin […] The post Najeriya da Majalisar Dinkin Duniya za su Kara Hada Kai Don Kare Hakkin Dan Adam Da Tallafawa Wadanda Rikice-rikice ya Shafa appeared first on GTR .

Najeriya da Majalisar Dinkin Duniya za su Kara Hada Kai Don Kare Hakkin Dan Adam Da Tallafawa Wadanda Rikice-rikice ya Shafa

Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa (Mai Ritaya), ya sake jaddada kudurin gwamnatin Najeriya na ci-gaba da bin dokokin jin-ƙai na ƙasa da ƙasa, tare da mutunta haƙƙin ɗan Adam a dukkan aiyukan rundunonin tsaro.

 

Ministan ya bayyana hakan ne a Shelkwatar Ma’aikatar Tsaro da ke Abuja, yayin wata ziyarar aiki da tawagar Mataimakiyar Babbar Sakatariyar Majalisar Ɗinkin Duniya kuma Jakadiyar Kare Haƙƙin wadanda Rikice-rikice suka shafa, Misis Najla Nassif Palma, ta kai masa.

 

 

Jagororin Siyasar Najeriya na Kokarin Maida Mulki na Gado – Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano

 

A yayin ganawar, Janar Musa ya yi wa tawagar karin bayani kan matakan da gwamnatin tarayya ta ɗauka domin magance wasu tsofaffin ƙalubale, da suka samo asali daga aiyukan wanzar da zaman lafiya da Najeriya ta gudanar a ƙasashen waje a shekarun baya.

 

Ya tabbatar wa tawagar cewa gwamnatin Najeriya ta samar da hanyoyin sadarwa da haɗin gwiwa domin hanzarta warware batutuwan da suka shafi wasu tsaffin ƙorafe-ƙorafe, musamman waɗanda suka danganci ikirarin alaƙar iyaye da yara da ake dangantawa da wasu aiyukan wanzar da zaman lafiya da aka gudanar a ƙasar Liberia, shekaru da dama da suka gabata.

 

Hotuna: Alkalanci Media ta Shirya Taron Wayar da Kai ga Malamai

 

A cewar Gwabin Musa, “Gwamnatin Najeriya na da aniyar tabbatar da gaskiya, adalci wajen warware duk wata matsala da ta shafi waɗannan batutuwa cikin gaskiya da mutunci”.

 

A nata jawabin tun da farko, Misis Najla Nassif Palma, ta baiyana cewa Majalisar Ɗinkin Duniya na nazarin wasu tsaffin shari’oi guda 42, da suka shafi waɗanda rikice-rikice ko aiyukan wanzar da zaman lafiya suka shafa.

 

NOA ta Fara Gangamin Wayar da Kan Matasan Jihar Bauchi Domin Inganta Tsaro

 

Ta buƙaci gwamnatin Najeriya da ta ci-gaba da bayar da haɗin kai domin tabbatar da adalci da samun mafita ga waɗanda lamarin ya shafa, tana mai cewa wasu daga cikinsu sun nuna sha’awar samun ɗan ƙasar Najeriya.

 

A ƙarshe sanarwar da mai taimaka wa Ministan kan yada labarai, Misis Leah Katung-Babatunde, ta aikowa GTR Hausa ta ce, ɓangarorin biyu sun amince da ƙara ƙarfafa haɗin guiwa a tsakaninsu ta hanyar shirya horaswa, Bitoci da sauran shirye-shiryen bunƙasa ƙwarewa, domin ƙara tabbatar da kare haƙƙin ɗan Adam a cikin aiyukan rundunonin tsaron Najeriya.

 

Tuni masu lura da al’amura suka fara hasashen cewa wannan haɗin guiwa zai taimaka wajen inganta martabar Najeriya a idon duniya, tare da ƙarfafa bin ƙa’idojin kare haƙƙin ɗan Adam da dokokin yaƙi a aiyukan tsaro da wanzar da zaman lafiya.

 

Gwamnatin Kano ta Dakatar da Bude Film House na Sultan Dake Unguwar Dorayi

The post Najeriya da Majalisar Dinkin Duniya za su Kara Hada Kai Don Kare Hakkin Dan Adam Da Tallafawa Wadanda Rikice-rikice ya Shafa appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow