Mata Masu Rawar Gala Sun Karɓi Addinin Musulunci a Hannun Hukumar Tace Fina-finai ta Kano

Daga Bashir Gasau.   Hukumar tace Fina-finai ta Jihar Kano ta jagorancin musuluntar da wasu ‘yan mata uku masu sana’ar Wasan Gala.   Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da Kakakin hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya aiko wa GTR Hausa inda ya ce Matan sun nuna ra’ayin kansu […] The post Mata Masu Rawar Gala Sun Karɓi Addinin Musulunci a Hannun Hukumar Tace Fina-finai ta Kano appeared first on GTR .

Mata Masu Rawar Gala Sun Karɓi Addinin Musulunci a Hannun Hukumar Tace Fina-finai ta Kano

Daga Bashir Gasau.

 

Hukumar tace Fina-finai ta Jihar Kano ta jagorancin musuluntar da wasu ‘yan mata uku masu sana’ar Wasan Gala.

 

Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da Kakakin hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya aiko wa GTR Hausa inda ya ce Matan sun nuna ra’ayin kansu na karɓar addinin na Musulunci.

 

Hotuna: Yadda Jam’iyyar ADC ta Tantance ‘Yan Takarar Gwamnonin Jihohi a Abuja

 

A cewar sanarwar, “An gudanar da wannan taro ne cikin wani biki na nuna farin ciki da Hukumarmu ta shirya a harabar dakin taronta, bisa jagorancin, Abba El-Mustapha”.

 

Mata Masu Rawar Gala Sun Karɓi Addinin Musulunci a Hannun Hukumar Tace Fina-finai ta Kano

 

Da yake jawabi a wajen taron, Abba El-mustapha ya bayyana wannan rana a matsayin rana ta musamman daga cikin ranaku mafi farin ciki da jin dadi a rayuwarsa.

 

Hotuna: Tawagar Hukumar Fansho a Ƙasar Afirka ta Kudu ta Kai Ziyara Matatar Dangote Dake Lagos

 

A cewarsa, “Wadannan Mata sun yanke wannan shawara ne a sakamakon ganin kyawawan halaye, zaman lafiya tare da juna, da kuma dabi’u nagari da suka gani daga kawayen su da abokan sana’arsu Musulmi a masana’antar ta nishadi.

 

Mata ukun da aka bayyana sunayensu da Dicson da Zara daga Jihar Adamawa, sai kuma Hannatu daga Jihar Gombe sun shafe tsawon lokaci suna sana’ar Gala.

 

Jirage 88 Sun yi Jigilar Maniyyatan Najeriya 35,038 Zuwa Kasar Saudiyya

 

Da take magana a madadin wadanda suka karɓi Musulunci, hannatu ta bayyana cewa kyawun addinin Musulunci, musamman yadda Musulmai ke rayuwa cikin zaman lafiya, Son juna da kyakkyawar mu’amala da jama’a, shi ne ya yi tasiri sosai wajen yanke shawararsu ta rungumar addinin na Musulunci.

 

PCACC Kano ta Fara Gudanar da Bincike Kan Tsohon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar

The post Mata Masu Rawar Gala Sun Karɓi Addinin Musulunci a Hannun Hukumar Tace Fina-finai ta Kano appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow