Masu Ruwa da Tsakin Unguwar Tudun Murtala ta Kano Sun Magance Matsalar Fadan Dabar Yankin Cikin Sauki

Daga Bashir Gasau.   Kwamitin Dattawan Unguwar Tudun Murtala ta ƙaramar hukumar Nassarawa da ke jihar Kano, sun gudanar da wani muhimmin taro tare da matasan da ke fadan daba da kuma shaye-shaye a yankin.   Kwamitin dattawan da ya jagoranci zaman ya ƙunshi tsohon shugaban Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON), Farfesa […] The post Masu Ruwa da Tsakin Unguwar Tudun Murtala ta Kano Sun Magance Matsalar Fadan Dabar Yankin Cikin Sauki appeared first on GTR .

Masu Ruwa da Tsakin Unguwar Tudun Murtala ta Kano Sun Magance Matsalar Fadan Dabar Yankin Cikin Sauki

Daga Bashir Gasau.

 

Kwamitin Dattawan Unguwar Tudun Murtala ta ƙaramar hukumar Nassarawa da ke jihar Kano, sun gudanar da wani muhimmin taro tare da matasan da ke fadan daba da kuma shaye-shaye a yankin.

 

Kwamitin dattawan da ya jagoranci zaman ya ƙunshi tsohon shugaban Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, Alhaji Yahaya Bagobiri, Farfesa Binyaminu, ACG Nasiru Isah rtd, inda suka tattauna da Matasan domin jin dalilan da suka haifar musu fadawa hanyoyin marasa kyau.

 

Kashe Manyan Jami’an Tsaro na Iya Jawo Rashin Ƙwarin Guiwa ga Abokan Aikinsu – Jabir Bichi

 

Kuma dai Matasan sun shaida musu cewa rashin aikin yi, munanan abokai, da kuma kyara da tsangwamar da al’umma ke nuna musu, a matsayin abinda ya haddasa musu fadawa hanyoyin marasa kyau.

 

Masu Ruwa da Tsakin Unguwar Tudun Murtala ta Kano Sun Magance Matsalar Fadan Dabar Yankin Cikin Sauki

 

A cewar Matasan, “Mafi yawancinmu bamu da aikin yi, wanda idan gari ya waye bamu san inda zamu tafi domin neman abinda za mu rufawa kansu asiri harma mu taimaki ‘Yan uwa da abokan arziki ba”.

 

Dattawa da Jami’an Tsaron Unguwar Tukuntawa Sun Dakile Fadan Daban da ya Taso

 

Mafari kenan da Kwamitin ya harhada kudi ya basu tallafi domin su je su yi jari, ta yadda za su dogara da kansu kuma su zama masu halaye na gari a cikin al’umma.

 

Masu Ruwa da Tsakin Unguwar Tudun Murtala ta Kano Sun Magance Matsalar Fadan Dabar Yankin Cikin Sauki

 

A hannu guda kwamitin ya sake tuntubar Shugaban Kamfanin Ammasco, Alhaji Mustapha Ado Muhammad, inda ya basu gurbin aiki na mutane Ashirin (20) a matsayin tasa gudunmawar, la’akari da yadda kamfanin yake a yankin.

 

Matsalar da Najeriya ke Ciki Laifin Talakawan Ƙasar ne – Abdulkarimu Daiyabu

 

Haka kuma ya wakilta masu Unguwanninsu da su sanya musu idanu don tabbatar da cewa sun yi amfani da abinda suka samu ta hanyar da ta dace.

 

A karshe Matasan sun baiyana godiyarsu ga wannan Kwamiti na Dattawan yankin, tare da alkawarin amfani da shawarwari da tallafin da aka basu, domin rayuwarsu da dada inganta kuma su zama Jakadun Unguwar na gari.

 

NBA (Ungogo Branch) Kano ta Bukaci Shugaba Tinubu ya Magance Matsalar Tsaron Najeriya

The post Masu Ruwa da Tsakin Unguwar Tudun Murtala ta Kano Sun Magance Matsalar Fadan Dabar Yankin Cikin Sauki appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow