Kungiyar Muryar Matan Arewa ta Sha Alwashin Wayar da Kan Al’umma Akan Illolin Shaye-shaye

Daga Abdurrashid B. Imam.   Kungiyar muryar matan arewa ƙarkashin jagorancin, Hajiya Binta Mukhtar Shata, ta sha alwashin wayar da kan al’umma illolin shaye-shaye a yankin Arewacin Najeriya.   Jami’ar yada labaran Ƙungiyar, Aisha Aliyu Isma’il, ce ta baiyana hakan a yayin tattakin haɗakar Kungiyoyin Mata da Matasa na jihar Kano albarkacin ranar yaki da […] The post Kungiyar Muryar Matan Arewa ta Sha Alwashin Wayar da Kan Al’umma Akan Illolin Shaye-shaye appeared first on GTR .

Kungiyar Muryar Matan Arewa ta Sha Alwashin Wayar da Kan Al’umma Akan Illolin Shaye-shaye












Daga Abdurrashid B. Imam.

 

Kungiyar muryar matan arewa ƙarkashin jagorancin, Hajiya Binta Mukhtar Shata, ta sha alwashin wayar da kan al’umma illolin shaye-shaye a yankin Arewacin Najeriya.

 

Jami’ar yada labaran Ƙungiyar, Aisha Aliyu Isma’il, ce ta baiyana hakan a yayin tattakin haɗakar Kungiyoyin Mata da Matasa na jihar Kano albarkacin ranar yaki da Sha da fataucin miyagun kwayoyi ta duniya, inda ta ce hakan zai taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalar shaye-shaye.

 

Rahoto: Shugaba Tinubu ya Sha Alwashin Kakkabe Matsalar Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi a Fadin Najeriya

 

A cewar Aisha, “Mun gudanar da wannan tattakin ne domin jan hankalin mahukunta, don daukan tsauraran matakai kan masu Sha da fataucin miyagun kwayoyi”.

 

Ta kuma ja hankalin al’umma da su kaucewa ta’ammali da kayan maye, saboda tarin illolin da ya ke haifarwa a cikin al’umma.

 

A nata bangaren Shugabar Kungiyar LESPADA, Ambasada Maryam Hassan, ta ce shaye-shaye baya maganin matsaloli illa sai kara dagula lamurah.

 

Hotuna: Yadda Bikin Nadin Garkuwan Kano da Kuma Sarkin Fulanin Ja’idinawan Kano ya Gudana

 

Adan haka ta yi fatan Mata da Matasa za su yi amfani da shawarwarin da suka basu a yayin wannan tattaki, ta yadda za a sami raguwar Sha da fataucin Miyagun kwayoyi daga nan zuwa Badi.

 

Daga bisani tsohon Mashawarcin gwamnan Kano kan harkokin Addinai, Honarabul Zikrullah Nura Ibrahim, ya ce akwai bukatar a hada hannu wajen yaki da matsalar shaye-shaye la’akari da yadda yake neman zama ruwan dare a tsakanin wannan al’umma.

 

Sun dai fara wannan tattaki ne daga kan titin Maiduguri zuwa kofar gidan gwamnatin jihar kano, inda dukkan bangarorin suka yi fatan kowa zai bada tasa gudunmawar domin gina al’umma mai lafiya, zaman lafiya, da kuma ci-gaba.

 

Najeriya da Burtaniya Sun Ƙarfafa Haɗin Guiwa Don Fuskantar Kalubalen Tsaro

The post Kungiyar Muryar Matan Arewa ta Sha Alwashin Wayar da Kan Al’umma Akan Illolin Shaye-shaye appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow