Kungiyar KCJF ta Shiryawa Mata Taron Wayar da Kai Kan Tsaftar Jiki a Yayin Al’ada

Daga Abdurrashid B. Imam.   Ƙungiyar Ƴan Jarida Masu Kishin Kano wato Kano Concerned Journalists Forum (KCJF), ta shirya taron wayar da kai ga dalibai Mata kan muhimman ilimi da fahimta game da lafiyar al’ada da hanyoyin kiyaye tsaftarta.   Shugabar Kungiyar, Aisha Ahmad Isma’il, ce ta jagoranci shirya taron a jiya Alhamis a Makarantar […] The post Kungiyar KCJF ta Shiryawa Mata Taron Wayar da Kai Kan Tsaftar Jiki a Yayin Al’ada appeared first on GTR .

Kungiyar KCJF ta Shiryawa Mata Taron Wayar da Kai Kan Tsaftar Jiki a Yayin Al’ada












Daga Abdurrashid B. Imam.

 

Ƙungiyar Ƴan Jarida Masu Kishin Kano wato Kano Concerned Journalists Forum (KCJF), ta shirya taron wayar da kai ga dalibai Mata kan muhimman ilimi da fahimta game da lafiyar al’ada da hanyoyin kiyaye tsaftarta.

 

Shugabar Kungiyar, Aisha Ahmad Isma’il, ce ta jagoranci shirya taron a jiya Alhamis a Makarantar Sakandiren ‘Yan Mata ta Magwan da ke birnin Kano.

 

Hotuna: Yadda Wata Kaza ta Kwana a “Cell”, Saboda yi wa Manomi Ta’adi a Gonarsa Dake Kano

 

Da take jawabi, Aisha Ahmad, ta ce sun shirya wannan taro ne da nufin ilmantar da ‘yan Mata kan yanayin al’ada, domin su bada tasu gudunmawar a matsayinsu na masu shiga lungu da saƙo suna ganin matsalolin da ke damun al’umma.

 

 

A cewarta, “Manufar bada wannan bita shine kara musu ilimi akan jinin al’ada, tallafa musu da Audugar Mata da kuma koya musu yadda za su yi amfani da ita, harma da yadda za su hada tasu ga wadanda basu da sararin siya”.

 

Hotuna: Jami’ar Sa’adu Zungur ta Bada Tallafin Kayan Aikin Ofis ga Caji Ofis Din Gadau na Jihar Bauchi

 

A nasa jawabin tsohon Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, ya bayyana wannan aiki a matsayin aikin da ake bukatar gwamnati, masu hannu da shuni da kuma daidaikun Mutane su kasance suna aiwatarwa.

 

Kungiyar KCJF ta Shiryawa Mata Taron Wayar da Kai Kan Tsaftar Jiki a Yayin Al'ada

 

Dakta Fatima Ibrahim Muktar, Likita ce a Asibitin Abdullahi Wase (Asibitin Nasarawa), ta gabatar da Mukala akan yanayin Jinin al’ada da kuma yadda mata za su kula da kansu, harma da yadda za su gane al’adar tasu bata dauke da wata Matsala.

 

Majalisar Wakilan Amurka ta Amince da Dakatar da Tallafin da Take Bawa Najeriya Kan Zargin Gallazawa Kiristoci

 

Shima Shugaban kungiyar ‘Yan Jaridu (NUJ) na kasa reshen jihar Kano, Kwamared Sulaiman Dederi, ya baiyana aikin da wannan kungiya ta yi a matsayin abin a yaba, la’akari da yadda take bada Gudunmawa a sha’anin rayuwar mata da sauran al’umma.

 

Ya kuma shawarci daliban da aka shirya taron domin su, su yi amfani da ilimin da suka samu domin inganta lafiyarsu da kuma ta ‘yan uwa da abokan arziki.

 

Cikakken Bayanin Hukumar Tace Fina-finai ta Kano Kan Musanta Labarin Soke Sana’ar Downloading

 

A karshe, Malama a tsangayar koyar da harshen Larabci na Jami’ar Bayero ta Kano, Amina Abdullahi Na’ibi, ta baiyana shirin a matsayin mataki me kyau da ya kamata sauran kungiyoyi su yi koyi, saboda muhimmancin ilimi da lafiyar Mata a cikin wannan al’umma.

 

Satar Mutane a Oriire: Majalisar Dattawan Najeriya ta Ware Naira Milyan 50 Don Tallafa wa Iyalan Wadanda Lamarin ya Shafa

The post Kungiyar KCJF ta Shiryawa Mata Taron Wayar da Kai Kan Tsaftar Jiki a Yayin Al’ada appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow