Ku Sanya Kishin Ƙasa a Zukatanku – Saƙon Barka da Sallar Tinubu ga Musulmin Najeriya

Daga Bashir Gasau.   Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya Musulmin kasar murnar ƙaramar Sallah (EidulFitr).   Mashawarcin Shugaban kasar kan yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ne ya sanar da sakon Tinubu ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya yi kira a garesu da su kasance masu kishin ƙasa ta hanyar […] The post Ku Sanya Kishin Ƙasa a Zukatanku – Saƙon Barka da Sallar Tinubu ga Musulmin Najeriya appeared first on GTR .

Ku Sanya Kishin Ƙasa a Zukatanku – Saƙon Barka da Sallar Tinubu ga Musulmin Najeriya

Daga Bashir Gasau.

 

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya Musulmin kasar murnar ƙaramar Sallah (EidulFitr).

 

Mashawarcin Shugaban kasar kan yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ne ya sanar da sakon Tinubu ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya yi kira a garesu da su kasance masu kishin ƙasa ta hanyar ƙara jajircewa wajen hidimtawa ƙasa da al’umma baki-ɗaya.

 

Manyan Abubuwan da Suka Faru Daga Safe Zuwa Daren Yau Alhamis a Yakin Iran da Kuma Amurka da Isra’ila 19=03=2026

 

Tinubu ya kuma buƙaci Musulmi da su ci-gaba da riƙe darussan watan Ramadan, musamman waɗanda suka shafi tsoron Allah, tausayi da haɗin kai tsakanin al’umma, harma ya horesu da su dinga taimakawa buƙata ba tare da la’akari da addini ba, domin ƙarfafa zumunci da haɗin kai a tsakanin ‘yan ƙasa.

 

A cewarsa, “Akwai darussa masu yawa da ya kamata a ɗauka daga Ramadan musamman a irin wannan lokaci, adan haka ina mai jaddada muhimmancin bin kyawawan halaye kamar sadaukarwa, juriya, alheri da jin-ƙai har bayan watan azumi”.

 

Daga bisani ya roƙi shugabannin addinin da su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa ƙasa addu’o’in zaman lafiya da ci-gaba, a inda ya jaddada ƙoƙarin gwamnatin na samar da yanayi mai kyau domin walwalar al’umma.

 

Lokutan Sallar Idi a Wasu Jihohin Najeriya

The post Ku Sanya Kishin Ƙasa a Zukatanku – Saƙon Barka da Sallar Tinubu ga Musulmin Najeriya appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow