Kotu ta Hana Gwamnatin Kano Ci-gaba da Ginin BOA PLAZA Dake Unguwar Farm Center

Daga Bashir Gasau.   Babbar kotun Jihar Kano Mai Lamba 11 da ke zaune a Miller Road, karkashin jagorancin Mai Shari’a, Justice Nasiru Saminu, ta hana gwamnatin Kano ci-gaba aikin ginin BOA PLAZA da ke Unguwar Farm Center.   Tunda fari dai Kamfanonin Jean B Project and property Development co. LTD da kuma G Empire […] The post Kotu ta Hana Gwamnatin Kano Ci-gaba da Ginin BOA PLAZA Dake Unguwar Farm Center appeared first on GTR .

Kotu ta Hana Gwamnatin Kano Ci-gaba da Ginin BOA PLAZA Dake Unguwar Farm Center












Daga Bashir Gasau.

 

Babbar kotun Jihar Kano Mai Lamba 11 da ke zaune a Miller Road, karkashin jagorancin Mai Shari’a, Justice Nasiru Saminu, ta hana gwamnatin Kano ci-gaba aikin ginin BOA PLAZA da ke Unguwar Farm Center.

 

Tunda fari dai Kamfanonin Jean B Project and property Development co. LTD da kuma G Empire Landmark Project LTD, ne suka yi karar gwamnatin Kano, Hukumar tsare birane (KNUPDA), bisa zargin mallake musu waje, tare da ci-gaba da aikin ginin wajen ba bisa ka’ida ba, adan haka suka shigar da karar domin a dakarar da aikin kuma a binciko wanda yake aikin.

 

Duk Sojan da Yaki Kashe Dan Ta’adda Saboda Jiran Umarni za mu Ɗauke Shi a Matsayin Dan Ta’adda – Ministan Tsaron Najeriya

 

Kuma dai a ranar 30 ga watan Yunin da ya gabata ne Mai shari’a, Nasiru Saminu, ya bada Umarnin dakatar da aikin ginin (Court Order), har sai an kammala shari’ar, harma ya ce dukkan bangarorin ciki har da wakilai su daina duk wani aiki a wajen.

 

Kotu ta Hana Gwamnatin Kano Ci-gaba da Ginin BOA PLAZA Dake Unguwar Farm Center

 

Toh sai dai kuma a ranar 7 ga watan Yulin da muke ciki ne lauyan masu kara Barista M N Duru (SAN), ya gabatar da kokensu a kotun kan cewa wadanda ake karar basu bi umarnin kotun ba domin sun ci gaba da ginin, lamarin da ya baiyana a matsayin Raina Kotu.

 

Hotuna: Yariman Saudiyya ya Karbi Bakuncin Firaministan Kasar Canada

 

A yayin zaman na Yau Alhamis, Lauyan masu kara Barista M N Duru (SAN), ya jaddada rokonsu na Kotun ta sanya a tsayar da ginin da akeyi a wajen har sai an kammala shari’ar, a inda lauyan gwamnatin Kano da kuma Hukumar tsara birane ta jihar (KNUPDA), Barista Ibrahim Abdullahi Sa’ad, yayi suka akan rokon, inda ya ce aikin yana kan ka’ida.

 

Kotu ta Hana Gwamnatin Kano Ci-gaba da Ginin BOA PLAZA Dake Unguwar Farm Center

 

Ko da Kotun ta sake waiwayar lauyan waɗanda ake kara kan batun bijirewa Umarninta na dakatar da aikin ginin, sai ya ce bashi da masaniya akan hakan.

 

Gamayyar Ƙungiyoyin Ɗaliban Jami’ar Aliko Dangote Sun Buƙaci Gwamnatin Kano ta Gaggauta Biyan Ma’aikatan Jami’ar Haƙƙoƙinsu

 

Bayan sauraron kowanne bangare, Alkalin ya umarci Babban Sakatare na Hukumar tsara birane (KNUPDA) da kuma Atoni Janar na Kano, su gurfana a gabanta a zama na gaba domin bada ba’asi kan ci-gaba da ginin.

 

A karshe Alkalin ya dage zaman zuwa ranar 17 ga watan Yulin da muke ciki, tare da gargadar Gwamnatin Kano da Hukumar tsara birane (KNUPDA), kan lallai su bi Umarnin Kotun.

 

Hukumar Alhazan Jihar Yobe ta Sanya Naira Miliyan 7.5 a Matsayin Kudin Aikin Hajjin Shekarar 2027

 

Bayan fitowa daga Kotun Lauyan masu kara, Barista M N Duru, ya ce tun kusan shekaru biyu ake wannan shari’a, wanda an so a sulhunta a tsakanin bangarorin amma ci-gaba da ginin ya kawo tsaiko.

 

Toh sai dai ko da muka yi kokarin jin ta bakin Lauyan wadanda ake kara, Barista Ibrahim Abdullahi Sa’ad, yace ba zai ce komai har sai nan gaba ko kuma bayan an kammala Shari’ar.

 

‘Yan Sandan Jihar Zamfara Sun Ceto Ma’aikacin INEC Tare da Kwato Shanu a Hannun ‘Yan Bindiga

The post Kotu ta Hana Gwamnatin Kano Ci-gaba da Ginin BOA PLAZA Dake Unguwar Farm Center appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow