Kotu ta Ci-gaba da Sauraron Shari’ar Zaben Fidda Gwanin Kujerar Gwamnan Jihar Nasarawa na Jam’iyyar ADC

Daga Kallamu Galadima Dambo.   A yau Alhamis ne Kotu ta ci-gaba da sauraron Shari’ar da tsohon Ministan Muhallin Najeriya, Barista Mohammed Hassan Abdullahi, ya yi karar Janar Angbozo Rtd, bisa zargin aringizo a zaben fidda gwani Kujerar Jam’iyyar ADC a jihar Nasarawa.   Barista Mohammed Hassan, ya garzaya Kotun ne a bisa zargin yin […] The post Kotu ta Ci-gaba da Sauraron Shari’ar Zaben Fidda Gwanin Kujerar Gwamnan Jihar Nasarawa na Jam’iyyar ADC appeared first on GTR .

Kotu ta Ci-gaba da Sauraron Shari’ar Zaben Fidda Gwanin Kujerar Gwamnan Jihar Nasarawa na Jam’iyyar ADC












Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

A yau Alhamis ne Kotu ta ci-gaba da sauraron Shari’ar da tsohon Ministan Muhallin Najeriya, Barista Mohammed Hassan Abdullahi, ya yi karar Janar Angbozo Rtd, bisa zargin aringizo a zaben fidda gwani Kujerar Jam’iyyar ADC a jihar Nasarawa.

 

Barista Mohammed Hassan, ya garzaya Kotun ne a bisa zargin yin aringizo a zaben fidda gwani na wasu yankuna a jihar Nasarawa, lamarin da yace lallai ya nemi hakkinsa.

 

Shugaba Tinubu ya Fadada Rundunonin Sojin Kasa Zuwa Rukuni 12 Tare da Daukar Sabbin Sojoji 28,000

 

Bayan sauraron bangarorin biyu, Kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 28 ga wannan watan Yulin da muke ciki domin ci-gaba da shari’ar.

 

Bayan fitowa daga kotun Lauyan Janar Angbozo, Barista Pius Akubo (SAN), ya ce zargin da masu kalubantar nasarar suke yi bashi da tushe ballantana Makama.

 

Mataimakin Shugaban Najeriya ya Tafi Ziyarar Aiki Jamhuriyar Benin

 

Shima Lauyan tsohon Ministan, Barista Muhammad Adamu Wamba, suna da yakinin kotu za ta dawo musu da nasarar su tunda su al’umma suka amince su shiga babban zaben shekarar 2027.

 

A karshe Barista Wamba, ya ja Hankali Matasa da sauran magoya bayan Jam’iyyar ADC da su hada-kai kasancewar dodo daya suke yiwa tsafi.

 

‘Yan Sandan Kano da Al’ummar Gari Sun Kama Gungun Wadanda Ake Zargi Sun Ƙware Wajen Fashin Adaidaita Sahun Mutane

The post Kotu ta Ci-gaba da Sauraron Shari’ar Zaben Fidda Gwanin Kujerar Gwamnan Jihar Nasarawa na Jam’iyyar ADC appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow