IHRC ta Bukaci Gwamnatin Najeriya ta Janye Karin Kudin Jarrabawar NECO

Daga Bashir Gasau.   Kungiyar kare haƙƙin dan adam ta International Human Rights Commission (IHRC-RFT), ta bukaci gwamnatin Najeriya ta janye karin kudin jarrabawar kammala babban Sakandire (NECO), da tayi zuwa Naira 50,000, wanda zai fara aiki daga shekarar 2027.   Daraktan kungiyar na Najeriya, Kaftin Abdullahi Bakoji Adamu (Rtd), ne ya sanar da hakan […] The post IHRC ta Bukaci Gwamnatin Najeriya ta Janye Karin Kudin Jarrabawar NECO appeared first on GTR .

IHRC ta Bukaci Gwamnatin Najeriya ta Janye Karin Kudin Jarrabawar NECO












Daga Bashir Gasau.

 

Kungiyar kare haƙƙin dan adam ta International Human Rights Commission (IHRC-RFT), ta bukaci gwamnatin Najeriya ta janye karin kudin jarrabawar kammala babban Sakandire (NECO), da tayi zuwa Naira 50,000, wanda zai fara aiki daga shekarar 2027.

 

Daraktan kungiyar na Najeriya, Kaftin Abdullahi Bakoji Adamu (Rtd), ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya ce aiwatar da wannan ƙarin a wannan lokaci na tsadar rayuwa zai raunana amincewar jama’a da ƙudirin gwamnati na faɗaɗa damar samun ilimi.

 

CAN ta Buƙaci Mahukuntan Najeriya su Ɗauki Matakan da za su Kawo Ƙarshen Garkuwa da Mutane

 

Harma ya ce zai haifar da rashin jin daɗin Milyoyin iyalai masu kaɗa ƙuri’a, wanda ka iya yin tasiri ga yanayin siyasa yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027.

 

A cewarsa, “Ilimi haƙƙi ne na ɗan Adam a ƙarkashin Mataki na 26 na Sanarwar Duniya kan Haƙƙin Dan Adam, haka kuma sashe na 18 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, ya ɗora wa gwamnati alhakin samar da daidaito da isassun damar samun ilimi a kowanne mataki”.

 

APC Sak Za mu yi a 2027 Domin Sakawa Gwamnan Kano Halascin da Yayi Mana – Al’ummar Wasu Garuruwan Ƙaramar Hukumar Ungogo

 

Bugu da kari ya ce Masana harkokin tsaro na ci-gaba da baiyana rashin samun ilimi, talauci, da ware matasa daga damar ci-gaba na daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da rashin tsaro, tsatstsauran ra’ayi, da sauran nau’ukan laifuka a Najeriya.

 

Adan haka ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin, Bola Ahmed Tinubu, da ta gaggauta janye wannan ƙarin kuɗi, tare da aiwatar da manufofin da za su faɗaɗa damar samun ilimi, kare iyalai masu ƙaramin ƙarfi, da kuma zuba jari wajen bunƙasa ilimin al’umma a matsayin hanya mafi inganci ta inganta tsaro da ci-gaban ƙasa.

 

Ranar Yawan Al’umma ta Duniya: Yawan Mutanen Duniya ya kai Bilyan 8.2 – Madawakin Muri

The post IHRC ta Bukaci Gwamnatin Najeriya ta Janye Karin Kudin Jarrabawar NECO appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow