Hukumar NDE Reshen Jihar Bauchi ta Fara Rijistar Mutane Don Koyar Dasu Sana’o’i Daban-daban

Daga Mu’azu Hardawa Bauchi.   Hukumar Samar da Aiyukan yi ta Najeriya reshen jihar Bauchi wato National Directorate of Employment (NDE), ta fara rijistar mutane ta yanar gizo domin koya musu Sana’o’i Daban-daban   Shugaban hukumar na jihar Bauchi, Alhaji Jamilu Adamu, ne ya tabbatar da hakan a yayin zantawarsa da manema labarai, inda ya […] The post Hukumar NDE Reshen Jihar Bauchi ta Fara Rijistar Mutane Don Koyar Dasu Sana’o’i Daban-daban appeared first on GTR .

Hukumar NDE Reshen Jihar Bauchi ta Fara Rijistar Mutane Don Koyar Dasu Sana’o’i Daban-daban












Daga Mu’azu Hardawa Bauchi.

 

Hukumar Samar da Aiyukan yi ta Najeriya reshen jihar Bauchi wato National Directorate of Employment (NDE), ta fara rijistar mutane ta yanar gizo domin koya musu Sana’o’i Daban-daban

 

Shugaban hukumar na jihar Bauchi, Alhaji Jamilu Adamu, ne ya tabbatar da hakan a yayin zantawarsa da manema labarai, inda ya ce manufar shirin shine don tallafawa mutane su koyi sana’o’in da za su dogara da Kansu harma su koya wa wasu.

 

Hotuna: Yadda AIG Garba Ahmed ya Sabunta Ginin Shelkwatar Rundunan ‘Yan Sandan Shiyya ta Daya (Zone One Kano)

 

A cewarsa, “Ana gudanar da shirin ne bisa tallafin Ministan samar da aiyukan yi na kasa, Alhaji Mohammed Maigari Dingyadi, a karkashin jagorancin shugaban hukumar NDE na Najeriya, Mista Silas Ali Agara”.

 

Ya kara da cewa an kaddamar da rijistar daliban ne a jiya Alhamis 23 ga watan Yuli, daga shekara 18 zuwa 45 ta shafin yanar gizo na “nderegistrationportal.ng” domin shiga sahun mutane dubu 21,824 da za su koyi sana’o’in a Jihohin Najeriya 36 da Abuja.

 

Ministan Ilimi ya Yabawa Shirin WOFAN–CDA SIBLING, ta Hanyar Jinjinawa Ƙoƙarin Inganta Ƙwarewar Ɗaliban Aikin Gona da Horo na Aikace-aikace

 

Bugu da kari ya ce wannan shine karo na Uku na shirin a karkashin jagorancin Shugaba, Bola Ahmed Tinubu, wanda aka yi masa lakabi da Renew Hope Employment Initiative (RHEI), inda za a dauki kowanne nau’in mutane Maza da Mata da masu bukata ta musamman daga dukkan mazabun kasar, domin basu horo na makonni 6 a fannin kasuwanci, Sana’a, Noma da Kiwo da sauran aiyukan dogaro da Kai.

 

Ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Arewa Tayi Alkawarin Horas da Mambobinta Dabarun Kasuwancin Zamani

 

Adan haka ya ce ga duk mai bukata ya tanadi katinsa na dan Kasa (NIMC) da kuma Email, ko ya ziyarci shagunan yanar gizo (Cafe) mafi kusa dashi don ayi masa rijistar, harma ya ce suna maraba da masu neman Karin haske game da yadda za a gudanar da wannan shiri.

 

A karshe ya ce za a dauki tsawon mako guda ana rijistar, a inda za a hada mutanen da suka sami nasarar shiga shirin a ofishin hukumar da ke Kofar Idi kusa da Masallacin Jumu’a na Malam Zubairu Madaki da ke garin Bauchi.

 

Kotu ta Ci-gaba da Sauraron Shari’ar Zaben Fidda Gwanin Kujerar Gwamnan Jihar Nasarawa na Jam’iyyar ADC

The post Hukumar NDE Reshen Jihar Bauchi ta Fara Rijistar Mutane Don Koyar Dasu Sana’o’i Daban-daban appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow