Harkokin Tsaro Ba Zai Kai ga Nasara ba Sai da Hadin Kan Al’umma – Birgediya Janar Abdussalam

Daga Sani Gazas, Damaturu.   Babban mai bawa Gwamnan Yobe shawara, kan harkokin tsaro na musamman, Birgediya Janar Dahiru Abdussalam, ya ce harkokin tsaro ba zai kai ga nasara ba sai da haɗin kan al’umma.   Birgediya Janar Dahiru, ya baiyana hakan ne a yayin zantawarsa da Wakilin GTR Hausa a jihar Yobe, inda ya […] The post Harkokin Tsaro Ba Zai Kai ga Nasara ba Sai da Hadin Kan Al’umma – Birgediya Janar Abdussalam appeared first on GTR .

Harkokin Tsaro Ba Zai Kai ga Nasara ba Sai da Hadin Kan Al’umma – Birgediya Janar Abdussalam












Daga Sani Gazas, Damaturu.

 

Babban mai bawa Gwamnan Yobe shawara, kan harkokin tsaro na musamman, Birgediya Janar Dahiru Abdussalam, ya ce harkokin tsaro ba zai kai ga nasara ba sai da haɗin kan al’umma.

 

Birgediya Janar Dahiru, ya baiyana hakan ne a yayin zantawarsa da Wakilin GTR Hausa a jihar Yobe, inda ya ce babu yadda za’a yi Jami’an tsaro su Kai ga nasarar kawar da ‘yan ta’adda da sauran Bara-gurbin da ke cikin mutane har sai an hada kai a tsakanin al’umma.

 

Sarkin Gumel, Alhaji Dakta Ahmed Muhammad, ya Rasu

 

A cewarsa, “Sanin kowa ne cewar a halin da ake ciki harkokin tsaro ya kusa daidaita a jihar ta Yobe, in banda wasu ‘yan hare-hare da aka samu daga wasu ‘yan ta’addan Boko Haram a yankunan ƙananan hukumomin Bursari, Geidam, Yunusari da Gujba, wanda su din ma tuni Sojoji da jami’an CJTF suka kawar da su”.

 

Shelkwatar Sojin Nijar ta Buƙaci Sojojin da Suka Gudu Daga Kasar a Lokacin Bore su Mika Kansu

 

Ya kara da cewa Yobe ta kasance jihar da ke da babbar iyaka Mai fadin gaske tsakaninta da Jamhuriyar Nijar, wadda hakan kan taimaka wa ‘yan ta’addan wajen rabewa su aikata ta’addancin su.

 

Adan haka ya ce ya zama wajibi al’umma su ci gaba da hada Kai da jami’an tsaro musamman ta wajen ba su rahoton duk wani motsin da basu gamsu dashi ba, harma ya bawa al’ummar jihar a bisa muhimmiyar rawar da suke takawa wajen hada Kai da jami’an tsaro wajen fallasa batagari.

 

Bai Kamata Malamai Su Dinga Kafurta Masu Yin Maulidi ba – Dan Azumi Gwarzo

 

Dangane da zaben ƙananan hukumomin da ya tunkaro a jihar, Birgediya Janar Abdussalam, ya bada tabbaci ga al’ummar jihar cewar kamar kowane lokaci a yanzu ma za’a gudanar dashi lami lafiya da yardar Ubangiji.

 

A ƙarshe ya ce yana da tabbacin cewar, gwamnan Jihar, Mai Mala Buni, ya yi tanadi mai kyau dangane da tsaron al’umma tare da taimakon Allah da Kuma taimakon jami’an tsaron da ke jihar.

 

Gwamnatin Jigawa da Kungiyar WOFAN Sun Ƙarfafa Haɗin Guiwa Kan Sauya Harkar Noma, Don Shigar da Mata da Matasa da Masu Bukata ta Musamman

The post Harkokin Tsaro Ba Zai Kai ga Nasara ba Sai da Hadin Kan Al’umma – Birgediya Janar Abdussalam appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow