Gwamnatin Yobe za ta Kashe Naira Milyan 460.8 Wajen Tallafawa Masu Tuyar Kosai dai Sauran Kananan Sana’o’i

Daga Sani Gazas Damaturu.   Gwamnatin Jihar Yobe ta amince da kashe naira Milyan 460,828,450.00, don tallafawa masu tuyar Kosai da sauran ƙananan sana’oi a mazabu 178 da ke fadin jihar.   An amince da hakan ne a yayin taron majalisar zartarwar Jihar wanda, Gwamna Mai Mala Buni, ya jagoranta a gidan gwamnati da ke […] The post Gwamnatin Yobe za ta Kashe Naira Milyan 460.8 Wajen Tallafawa Masu Tuyar Kosai dai Sauran Kananan Sana’o’i appeared first on GTR .

Gwamnatin Yobe za ta Kashe Naira Milyan 460.8 Wajen Tallafawa Masu Tuyar Kosai dai Sauran Kananan Sana’o’i












Daga Sani Gazas Damaturu.

 

Gwamnatin Jihar Yobe ta amince da kashe naira Milyan 460,828,450.00, don tallafawa masu tuyar Kosai da sauran ƙananan sana’oi a mazabu 178 da ke fadin jihar.

 

An amince da hakan ne a yayin taron majalisar zartarwar Jihar wanda, Gwamna Mai Mala Buni, ya jagoranta a gidan gwamnati da ke Damaturu.

 

Cikakken Rahoton Yadda Kaza ta Kwana a “Cell”, Saboda yi wa Manomi Ta’adi a Gonarsa Dake Kano

 

Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan taron, kwamishinan harkokin cikin gida da al’adu, Alhaji Abdullahi Bego, ya ce matakin da aka dauka an yi shi ne don tallafawa matan da ke gudanar da kananan kasuwanci da sana’o’i ta hanyar samar da muhimman abubuwa don habaka rayuwarsu.

 

A cewarsa, “Za a raba buhunan wake 1,780 mai nauyin kilogiram 50, tare da man girki, murhu na zamani maras hayaki, kayan girki da kayan kicin, wadanda ma’aikatar samar da arziki da samar da aiki ta riga ta siyo kuma ta adana su”.

 

Addu’a Kadai ba Zata yi Maganin Matsalolin Najeriya ba, Sai an Daina Abubuwa 5 – Abdulkarimu Daiyabu

 

Haka kuma majalisar ta amince da ware naira milyan 364,475,000.00 don siyen injunan nika (Yamaha GX 390) guda 1,000 don tallafawa mutane a fadin jihar.

 

Dadin dadawa an ware Naira Bilyan 73.32 don gudanar da aiyuka a sassa masu muhimmanci na tattalin arzikin jihar, wanda ya kunshi Bilyan 28.53 don siyan kayan aikin noma don shirin karfafawa manoma guiwa na shekarar 2026, Naira bilyan 23.97 don manyan aiyukan hanya guda biyu, da kuma ware kudade don harkokin gidaje, kasuwanni da sauran aiyukan ababen more rayuwa.

 

WOFAN ta Kaddamar da Gadar Tsallaka Titi, Rijiyar Burtsatse Mai Amfani da Hasken Rana da Sabuwar Hanya Domin Bunƙasa Rayuwar Al’ummar Danbare da Maƙwabta Dake Kano

The post Gwamnatin Yobe za ta Kashe Naira Milyan 460.8 Wajen Tallafawa Masu Tuyar Kosai dai Sauran Kananan Sana’o’i appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow