Gwamnatin Singapore za ta Tallafawa Kowane Yaro da Sama da Naira Milyan 90

Daga Bashir Gasau.   Gwamnatin ƙasar Singapore ta sanar da sabon tsarin tallafa wa iyalai, wanda zai sa kowanne yaro ɗan ƙasar da ya cancanta samun tallafin kusan S$70,000, kwatankwacin Naira Milyan 94, daga haihuwa har zuwa Shekaru 17.   Firaministan ƙasar, Lawrence Wong, ne ya baiyana hakan a jawabinsa na National Day Rally da […] The post Gwamnatin Singapore za ta Tallafawa Kowane Yaro da Sama da Naira Milyan 90 appeared first on GTR .

Gwamnatin Singapore za ta Tallafawa Kowane Yaro da Sama da Naira Milyan 90












Daga Bashir Gasau.

 

Gwamnatin ƙasar Singapore ta sanar da sabon tsarin tallafa wa iyalai, wanda zai sa kowanne yaro ɗan ƙasar da ya cancanta samun tallafin kusan S$70,000, kwatankwacin Naira Milyan 94, daga haihuwa har zuwa Shekaru 17.

 

Firaministan ƙasar, Lawrence Wong, ne ya baiyana hakan a jawabinsa na National Day Rally da ya gabatar a jiya Lahadi, 23 ga watan Agustan shekarar 2026, inda ya ce sabon shirin “SG Child Support Package” ya ƙunshi tallafi daban-daban da gwamnati za ta rika bawa iyalai domin rage musu nauyin kula da ’ya’yansu.

 

A ƙarƙashin shirin, za a bai wa kowanne yaro S$10,000 a matsayin tallafin haihuwa, yayin da S$32,000 za a bayar a matsayin Child Credits.

 

Sarkin Musulmin Najeriya ya Cika Shekaru 70 da Haihuwa

 

Haka kuma, gwamnati za ta ware S$5,000 a matsayin tallafin Child Development Account (CDA), tare da ƙarin tallafin gwamnati da zai kai S$5,000.

 

Bugu da ƙari, za a ƙara S$10,000 a asusun karatun yaro idan ya kai shekara 17.

 

Gwamnatin ta ce idan aka haɗa waɗannan tallafe-tallafen da sauran shirye-shiryen da ake da su, ciki har da S$5,000 na MediSave Grant for Newborns da kuma tallafin Edusave na shekara-shekara, jimillar tallafin da kowane yaro zai samu ya kai kusan S$70,000.

 

Wannan ya haura tallafin da iyaye ke samu a yanzu, wanda yake tsakanin S$27,500 zuwa S$56,500, gwargwadon yawan ’ya’yan da suke da su.

 

Tinubu ya ce Gwamnatinsa ta Cika Alkawuran da ta Ɗauka a Lokacin Yakin Neman Zaɓen 2023

 

Ana sa ran sabon tsarin zai amfani sama da yara 610,000 daga gidaje kusan 380,000.

 

A cewar gwamnatin, S$10,000 na tallafin haihuwa za a biya shi kashi biyu cikin shekarar farko bayan haihuwar yaro, yayin da za a rika bayar da S$2,000 a duk shekara daga lokacin da yaro ya cika shekara ɗaya har zuwa shekara 16.

 

Haka kuma, lokacin da yaro ya kai shekara 17, za a ƙara masa S$10,000 a asusun karatunsa na gaba da sakandare.

 

Zantawar GTR Hausa da Kwamishinan Yan Sandan Jihar Neja Kan Sace Masallata a Masallacin Jumu’a

 

Matakin na daga cikin ƙoƙarin Singapore na ƙarfafa haihuwar ’ya’ya, yayin da ƙasar ke fuskantar raguwar yawan haihuwa.

 

Firaminista Wong ya ce tallafa wa iyalai da ’yan ƙasar na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin ƙasar ta sanya a gaba.

 

Sai dai, ba wai za a bai wa ma’aurata Naira miliyan 94 a tsabar kuɗi lokaci guda ba. Adadin ya ƙunshi jimillar fa’idodin tallafin gwamnati da kowane yaro zai samu daga haihuwa har zuwa shekara 17.

 

Vanguard

 

SERAP ta Buƙaci INEC ta Bayyana Adadin Kuɗaɗen da Jam’iyyu za su Kashe a Yaƙin Neman Zaɓen 2027

The post Gwamnatin Singapore za ta Tallafawa Kowane Yaro da Sama da Naira Milyan 90 appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow