Gwamnatin Neja da Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sun Rage Matsalar Tsaro da Kaso me Yawa – VGN

Daga Kallamu Galadima Dambo.   Kungiyar ‘Yan Sintiri ta Najeriya reshen jihar Neja, (Vigilante Group of Nigeria), ta ce gwamnatin Neja da hadin guiwar rundunar ‘Yan Sandan jihar, sun sami nasarar rage kaso me yawa na matsalar tsaron da ta addabi jihar.   Kwamandan Ƙungiyar na jihar Neja, Nasiru Muhammad Manta, ne ya baiyana hakan […] The post Gwamnatin Neja da Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sun Rage Matsalar Tsaro da Kaso me Yawa – VGN appeared first on GTR .

Gwamnatin Neja da Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sun Rage Matsalar Tsaro da Kaso me Yawa – VGN

Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

Kungiyar ‘Yan Sintiri ta Najeriya reshen jihar Neja, (Vigilante Group of Nigeria), ta ce gwamnatin Neja da hadin guiwar rundunar ‘Yan Sandan jihar, sun sami nasarar rage kaso me yawa na matsalar tsaron da ta addabi jihar.

 

Kwamandan Ƙungiyar na jihar Neja, Nasiru Muhammad Manta, ne ya baiyana hakan a yayin zantawar sa da GTR Hausa, a lokacin da yake tsokaci kan cikar gwamnan Neja, Muhammad Umar Bago, shekaru Uku akan Karagar Mulki.

 

Ci-gaban Zantawar GTR Hausa da Ministan Tsaron Najeriya, Christopher Gwabin Musa

 

A cewar Manta, “Babu shakka an sami raguwar matsalar tsaro sosai a jihar Neja a sakamakon kokarin gwamnatin Umar Bago da kuma Kwamishinan ‘yan sandan jihar, ta fuskoki da dama”.

 

Ya kuma danganta kokarin nasu da abinda ya haddasa raguwar Mutane a wuraren kula da ‘Yan gudun hijira (IDP’s Camp), da ke sassan jihar.

 

Chief Nwanyanwu ya Zama Dan Takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar ZLP

 

Dadin dadawa ya kuma baiyana yadda suma suka bada gagarumar gudunmawa a wannan nasara, ta yadda aka dinga yakar ‘Yan ta’addar tare da su ba tare da tsoro ko gajiyawa ba.

 

A hannu guda ya ce a shirye suke wajen kafa Sansasononi a dukkan wuraren da ke fuskantar barazanar matsalar tsaro, domin ganin an hada hannu wajen fatattakarsu a lungu da saƙo na jihar.

 

Amfani da Sashe na Biyu na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya Zai Magance Matsalar Tsaron Ƙasar – Tsohon Mataimakin Jakadan Majalisar Ɗinkin Duniya

 

A ƙarshe ya yabawa gwamnatin Bago da na ƙananan hukumomin jihar Neja, a bisa yadda suke basu tallafin kudi da kayan aiki a kowanne Wata, saboda kara musu ƙwarin guiwar aikin da suke yi don kaunar al’ummarsu.

 

Hotuna: Gidauniyar Darul Erkam ta Bawa Marasa Ƙarfi Tallafin Nama ta Hannun GMBNI

The post Gwamnatin Neja da Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sun Rage Matsalar Tsaro da Kaso me Yawa – VGN appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow