Gwamnatin Bauchi ta Kaddamar da Jami’an Sintiri 2100 Don Inganta Tsaron Dazuka da Yankunan Karkara

Daga Muazu Hardawa Bauchi.   Gwamnatin jihar Bauchi ƙarkashin jagorancin gwamna Bala Abdulkadir Mohammed, (Kauran Daular Usmaniyya), ta horas da matasa 2170 don Shiga aikin Sintirin samar da tsaro da zaman lafiya a dazuka da yankunan karkarar jihar.   Da yake jawabi a lokacin bikin yaye matasan a madadin Gwamnan jihar, mataimakinsa, Honarabul Muhammad Auwal […] The post Gwamnatin Bauchi ta Kaddamar da Jami’an Sintiri 2100 Don Inganta Tsaron Dazuka da Yankunan Karkara appeared first on GTR .

Gwamnatin Bauchi ta Kaddamar da Jami’an Sintiri 2100 Don Inganta Tsaron Dazuka da Yankunan Karkara












Daga Muazu Hardawa Bauchi.

 

Gwamnatin jihar Bauchi ƙarkashin jagorancin gwamna Bala Abdulkadir Mohammed, (Kauran Daular Usmaniyya), ta horas da matasa 2170 don Shiga aikin Sintirin samar da tsaro da zaman lafiya a dazuka da yankunan karkarar jihar.

 

Da yake jawabi a lokacin bikin yaye matasan a madadin Gwamnan jihar, mataimakinsa, Honarabul Muhammad Auwal Jatau, ya ce matakin ya biyo bayan ganin girman kalubalen da ake fuskanta na lalata gandun daji da samun masaukai da bata gari ke yi.

 

Zazzafan Martanin Jam’iyyar ADC Kan Abubuwan da Suka Faru a Zaben Jihar Ekiti

 

Adan haka aka dauki matasan tare da basu horo na musamman na tsawon makonni a cibiyar horas da ‘yan sanda da ke Yalwan Tudu, inda ya gargaɗi sabbin jami’an da su kasance masu ladabi da nuna kwarewa wajen gudanar da aiyukansu ta hanyar gujewa duk wani abu da zai iya rage martabar su ko amincewar jama’a a kan su.

 

Gwamnatin Bauchi ta Kaddamar da Jami'an Sintiri 2100 Don Inganta Tsaron Dazuka da Yankunan Karkara

 

A cewarsa, “Gwamnatinmu ta bayar da umarnin kirkiro wannan shiri ne a sakamakon kudirinmu na kare gandun daji daga aiyukan ‘yan bindiga, musamman a wuraren da ake hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba”.

 

Gwamnatin Kano ta Rufe Makarantun Koyar da Aikin Lafiya Guda Biyu

 

Ya kuma bukaci jami’an da su yi aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro na gwamnati, domin tabbatar da samun ingantaccen tsaro da zaman lafiya a fadin jihar.

 

DIG Sani Muhammad (mai ritaya), shine Kwamishinan Harkokin Tsaron cikin gida kuma Babban Mai Bawa Gwamna Shawara kan harkokin Tsaro, ya ce an tsara wannan shiri ne domin inganta tsarin tsaro da ya dogara da al’umma tare da kara tabbatar da tsaron jama’a.

 

Dalilai Uku ne Suka Kara Ta’azzara Matsalar Tsaron Najeriya – Jabir Bichi

 

Shima Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani Omolori Aliyu, wanda DCP Musa M. Bulus, ya wakilta, ya yaba wa kokarin gwamnatin jihar wajen inganta tsaro, yana mai baiyana daukar sabbin jami’an a matsayin wani muhimmin mataki na karfafa tsaro a matakin birni da yankunan karkara.

 

Ya kuma tunatar da jami’an muhimmancin mutunta hakkin dan Adam da yin aiki bisa bin tanadin doka, da kuma ci-gaba da hadin guiwa da sauran hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

 

Har Gobe Babu Mu Babu Sulhu da ‘Yan Bindiga – Gwamnatin Zamfara

 

A karshe babban Sakatare kuma shugaban hada kan kungiyoyin tsaro na jihar Bauchi, Alhaji Umar Aliyu Shayi, ya baiyana daukar matasan a matsayin babbar nasara a wannan gwamnatin wacce a kullum take maida hankali wajen kare rayuka da dukiyoyin mutane.

 

Taron ya gudana ne a ranar Asabar din da ta gabata, a dandamalin fareti na makarantar horas da kananun ‘Yan Sanda (PTS) da ke jihar, inda ya sami halartar Jami’ai daga hukumomin tsaro, Sarakunan gargajiya da Jami’an gwamnati a matakai daban-daban da dai sauransu.

 

Akwai Buƙatar Musulmi da Kirista su Hada Hannu Wajen Koyar da Ilimin Addinansu a Makarantun Firamare da Sakandiren Arewacin Najeriya – Rabaran Kunama

The post Gwamnatin Bauchi ta Kaddamar da Jami’an Sintiri 2100 Don Inganta Tsaron Dazuka da Yankunan Karkara appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow