Gwamnan Kano ya Dakatar da Shugabar Hukumar Tsara Birane (KNUPDA)

Daga Bushira Aminu.   A kokarinsa na gyara taswirar Jihar Kano, Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da shugabar hukumar tsara birane (KNUPDA), Arc. Hauwa Hassan Tudun-wada.   Sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim, ne ya sanar da hakan a lokacin da yake ƙaddamar da wani kwamiti na mutane bakwai, da zai bibiyi yadda […] The post Gwamnan Kano ya Dakatar da Shugabar Hukumar Tsara Birane (KNUPDA) appeared first on GTR .

Gwamnan Kano ya Dakatar da Shugabar Hukumar Tsara Birane (KNUPDA)

Daga Bushira Aminu.

 

A kokarinsa na gyara taswirar Jihar Kano, Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da shugabar hukumar tsara birane (KNUPDA), Arc. Hauwa Hassan Tudun-wada.

 

Sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim, ne ya sanar da hakan a lokacin da yake ƙaddamar da wani kwamiti na mutane bakwai, da zai bibiyi yadda ake take dokokin tsara birane da yin gine-gine ba bisa ka’ida ba a jihar.

 

Jam’iyyar Action Alliance ce Jirgin Fiton Talakawan Najeriya – Ma’ajin Jam’iyyar na Kasa

 

A cewar Umar Faruk, “Rashin bin dokokin tsara birane da kula da gine-gine ya zama babban kalubale a jihar, lamarin da ke kawo cikas ga ƙoƙarin gwamnati na samar da ingantaccen tsarin birane da bunƙasa ababen more rayuwa da kuma kyautata yanayin birnin Kano”.

 

Mafari kenan da yace an kafa kwamitin domin gudanar da cikakken bincike kan ayyukan hukumar tsara birane, tare da gano dalilan da ke haddasa ci-gaba da take dokokin tsara birane.

 

Rasuwar Janar Rabe Babbar Izina ce ga Gwamnati da Talakawan Najeriya – Dakta Yahuza Getso

 

Sanarwar ta kuma ce wannan wani mataki ne na tabbatar da gaskiya da adalci a binciken, adan haka gwamnan ya umarci shugabar hukumar da daraktan sashen zane-zane na hukumar su ajiye aikinsu na wucin gadi har sai an kammala binciken.

 

A karshe sanarwar ta ce Shugaban hukumar KANGIS, Dakta Aliyu Dalhatu Sani, ne shugaban kwamitin, a yayin da Barista Rahma Malam Alhaji ta kasance Sakatariyar kwamitin.

 

Hakimin Kura ta Kano ya Kawo Ƙarshen Rikicin Filin Al’ummar Unguwar Dalili

The post Gwamnan Kano ya Dakatar da Shugabar Hukumar Tsara Birane (KNUPDA) appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow