GCHN ta Buƙaci Gwamnatin Kano ta Bincika Zargin Karbe Takardun Daukar Aiki na Mutane 1,163

Daga Bashir Gasau.   Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Rights Network a Najeriya (GCHN), ta buƙaci gwamnatin jihar Kano ta yi gaggawar bincike tare da ɗaukar mataki kan yadda ake zargin an karɓe takardun ɗaukar aiki (Offer Permanent and Pensionable Appointment) a fannin koyarwa a makarantun lafiya, tun gabanin su […] The post GCHN ta Buƙaci Gwamnatin Kano ta Bincika Zargin Karbe Takardun Daukar Aiki na Mutane 1,163 appeared first on GTR .

GCHN ta Buƙaci Gwamnatin Kano ta Bincika Zargin Karbe Takardun Daukar Aiki na Mutane 1,163












Daga Bashir Gasau.

 

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Rights Network a Najeriya (GCHN), ta buƙaci gwamnatin jihar Kano ta yi gaggawar bincike tare da ɗaukar mataki kan yadda ake zargin an karɓe takardun ɗaukar aiki (Offer Permanent and Pensionable Appointment) a fannin koyarwa a makarantun lafiya, tun gabanin su fara aiki.

 

Babban Daraktan ƙungiyar a Najeriya, Ambasada Ƙaribu Yahaya Lawan Kabara, ne ya bayyana hakan bayan da suka karɓi ƙorafi daga wajen wasu daga cikin malaman da ake shirin yi wa ta leƙo ta koma akan aikin da aka basu.

 

Zan Dawo da Tallafin Man Fetur Idan na Lashe Zaɓen 2027 – Atiku Abubakar

 

A cewar sa, “Aƙalla Malamai 1,163, ne gwamnatin jihar Kano ta baiwa takardun ɗaukar aiki da za su koyar a makarantun kiwon lafiya, amma daga bisani aka kirawo su aka karɓe takardun ba tare da sun fara aiki ba, lamarin da ya jefa su cikin damuwa a sakamakon yadda ake ƙokarin soke batun ɗaukar aikin gaba ɗaya”.

 

GCHN ta Buƙaci Gwamnatin Kano ta Bincika Zargin Karbe Takardun Daukar Aiki na Mutane 1,163

 

Ambasada Ƙaribu ya kara da cewa yanzu haka akwai tarin waɗanda aka karɓe takardun ɗaukar aikin da suka shigar da ƙorafin su a babban ofishin ƙungiyar, domin a shige musu gaba kan lamarin.

 

Ba Don Tinubu ya Cire Tallafin Man Fetur ba da Tuni Lita ta Kai 3,000 – Ministan Kudin Najeriya

 

Adan haka suka rubuta takardu zuwa ga ofishin Shugabar Ma’aikatan jihar Kano, Hajiya Bilkisu Mai Mota, domin jin ba’asi kan zargin soke ɗaukar aikin ga mutane 1,163, domin gujewa take musu haƙƙi.

 

GCHN ta Buƙaci Gwamnatin Kano ta Bincika Zargin Karbe Takardun Daukar Aiki na Mutane 1,163

 

Kabara ya kuma ce a takardun da suka turawa ofishin Shugabar Ma’aikatan, suna buƙatar bayanai kan ingancin takardun ɗaukar aikin da aka baiwa mutanen a baya aka karbe, tunda an tabbatar da cewa sun fito ne daga gwamnatin Kano.

 

Siyasa ce ta Sanya Aka Canja ni ba Doka ba – Martanin Mataimakin Gwamnan Kebbi

 

Ya kuma ce bayan ofishin Shugabar Ma’aikatan sun rubuta takardun zuwa ga ofisoshi guda biyar (5), da suka haɗar da Ofishin Gwamnan Kano, Anti Corruption, Civil Service, Technical Board, domin sanar da su wannan matsala.

 

Dadin dadawa Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya yi gaggawar ɗaukar matakan da suka dace a kan wannan lamari, domin tabbatar da adalci ga mutanen da ake shirin takewa haƙƙi, wanda ya ce watsi da shi ka iya cutar da siyasar gwamnan Kano da kuma gwamnatin sa, tare da kawo wa Kano talauci da ƙara haifar da masu zaman banza a gari, da kuma aikata laifuka.

 

‘Ya’yan Malam Ibrahim Dan’azumi Gombe Biyu ne Suka zo na Ɗaya a Musabakar Alƙur’ani ta Duniya – Farfesa Pantami

 

A ƙarshe ya ce ya zama wajibi Gwamnatin jihar ta ɗauki matakan da suka dace a kan wannan al’amari matukar da gaske ne tana kishin al’ummar ta da kuma kare martabar su, domin baiwa mutanen aiki ka iya taimaka wa wajen rage rashin aikin yi a tsakanin matasa da ma sauran al’ummar jihar.

 

Wajibi Gwamnatin Sokoto ta Hukunta

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow