Gamayyar Ƙungiyoyin Ɗaliban Jami’ar Aliko Dangote Sun Buƙaci Gwamnatin Kano ta Gaggauta Biyan Ma’aikatan Jami’ar Haƙƙoƙinsu

Daga Usman Hamza, Kano.   Gamayyar Ƙungiyoyin Ɗaliban Jami’ar Aliko Dangote da ke Wudil ta Jihar Kano, sun yi kira ga Gwamnatin Jihar da ta gaggauta biyan kuɗaɗen alawus da ƙarin albashin da ta amince da su tun kusan watanni bakwai da suka gabata.   Kungiyoyin sun shaidawa GTR Hausa cewa ci-gaba da jinkirta biyan […] The post Gamayyar Ƙungiyoyin Ɗaliban Jami’ar Aliko Dangote Sun Buƙaci Gwamnatin Kano ta Gaggauta Biyan Ma’aikatan Jami’ar Haƙƙoƙinsu appeared first on GTR .

Gamayyar Ƙungiyoyin Ɗaliban Jami’ar Aliko Dangote Sun Buƙaci Gwamnatin Kano ta Gaggauta Biyan Ma’aikatan Jami’ar Haƙƙoƙinsu












Daga Usman Hamza, Kano.

 

Gamayyar Ƙungiyoyin Ɗaliban Jami’ar Aliko Dangote da ke Wudil ta Jihar Kano, sun yi kira ga Gwamnatin Jihar da ta gaggauta biyan kuɗaɗen alawus da ƙarin albashin da ta amince da su tun kusan watanni bakwai da suka gabata.

 

Kungiyoyin sun shaidawa GTR Hausa cewa ci-gaba da jinkirta biyan kuɗaɗen na jefa ma’aikatan jami’ar cikin ƙunci.

 

Hukumar Alhazan Jihar Yobe ta Sanya Naira Miliyan 7.5 a Matsayin Kudin Aikin Hajjin Shekarar 2027

 

A cewarsu, “Abubuwan da gwamnatin ta amince da su sun haɗar da ƙarin albashi na kashi 25 zuwa 35 cikin ɗari ga ma’aikata, wanda jimillar kuɗin ya kai kimanin naira Bilyan 1.6 da za’a biya a cikin watanni huɗu, sai Earned Academic Allowance (EAA) ga mambobin ASUU, da kashi 50 cikin ɗari na Hazard Allowance da Student-Technology Ratio (STR) ga ma’aikatan fasaha, tare da aiwatar da ƙarin albashi ga dukkan ma’aikatan jami’ar”.

 

‘Yan Sandan Jihar Zamfara Sun Ceto Ma’aikacin INEC Tare da Kwato Shanu a Hannun ‘Yan Bindiga

 

Sun kara da cewa duk da gwamnatin ta amince da waɗannan haƙƙoƙi tun watanni bakwai da suka gabata, wanda kuma tuni ma’aikatan Jami’ar Northwest Kano sun riga sun karɓi irin waɗannan kuɗaɗe tun kafin watan Azumin Ramadan, amma su har yanzu ba’a fara biyan na Jami’ar Aliko Dangote ba, lamarin da ya sa suke neman a yi wa malamasu da dukkan ma’aikatan jami’ar irin wannan adalci.

 

A karshe sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ta cika alƙawarin da ta ɗauka ta hanyar sakin kuɗaɗen da aka amince da su domin a biya ma’aikatan jami’ar cikin gaggawa, suna mai jaddada cewa hakan zai ƙara musu ƙwarin guiwa tare da inganta harkokin koyarwa, bincike da gudanarwar jami’ar.

 

Zan Tabbatar ADC ta yi wa Sauran Jam’iyyu Fintinkau a Kano – Honarabul Umar Kwalwa

The post Gamayyar Ƙungiyoyin Ɗaliban Jami’ar Aliko Dangote Sun Buƙaci Gwamnatin Kano ta Gaggauta Biyan Ma’aikatan Jami’ar Haƙƙoƙinsu appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow