Firaministan Indiya ya Gayyaci Tinubu Taron BRICS

Daga Bashir Gasau.   Firaministan Indiya, Narendra Modi, ya gaiyaci Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zuwa taron ƙasashen BRICS na bana, a wani mataki na ƙarfafa haɗin gwiwa a fannoni daban-daban tsakanin ƙasashen biyu.   Gaiyatar na zuwa ne bayan Najeriya ta shiga ƙungiyar a matsayin abokiyar hulɗa a 2025, duk da har yanzu ba […] The post Firaministan Indiya ya Gayyaci Tinubu Taron BRICS appeared first on GTR .

Firaministan Indiya ya Gayyaci Tinubu Taron BRICS


















Daga Bashir Gasau.

 

Firaministan Indiya, Narendra Modi, ya gaiyaci Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zuwa taron ƙasashen BRICS na bana, a wani mataki na ƙarfafa haɗin gwiwa a fannoni daban-daban tsakanin ƙasashen biyu.

 

Gaiyatar na zuwa ne bayan Najeriya ta shiga ƙungiyar a matsayin abokiyar hulɗa a 2025, duk da har yanzu ba cikakkiyar mamba ba ce, amma tana halartar wasu tarurruka da shirye-shiryen ƙungiyar.

 

NSA Nuhu Ribadu ya Jagoranci Manyan Jami’an Najeriya Zuwa Tattaunawar Tsaro da Amurka

 

Masana na kallon gaiyatar a matsayin wata dama da Najeriya za ta yi amfani da ita wajen bunƙasa cinikayya da zuba jari da haɗin guiwar fasaha da Indiya da sauran ƙasashe masu tasowa.

 

Babban Jami’in Diflomasiyyar Indiya a Najeriya, Abhishek Singh, ya ce haɗin guiwar ƙasashen biyu ya wuce kasuwanci kawai, har ma da fannonin makamashi da tsaro da lafiya da noma da fasaha da kuma harkokin tsaron teku.

 

BBC Hausa.

 

Gwamnatin Najeriya ta Sanar da Kamfanonin Jiragen da za ta yi Amfani da su a Aikin Hajjin 2027

The post Firaministan Indiya ya Gayyaci Tinubu Taron BRICS appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow