Fadar Sarkin Musulmi ta Aiyana Gobe Lahadi a Matsayin Ranar 1 Ga Watan Zulqi’ida na Shekarar 1447

Daga Bashir Gasau.   Fadar Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta aiyana gobe Lahadi a matsayin ranar 1 ga watan Zulqi’ida na shekarar 1447, bayan hijira.   Sarkin Musulmin ya sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin harkokin addinin musulunci na fadar, Farfesa Sambo wali Junaidu (Wazirin […] The post Fadar Sarkin Musulmi ta Aiyana Gobe Lahadi a Matsayin Ranar 1 Ga Watan Zulqi’ida na Shekarar 1447 appeared first on GTR .

Fadar Sarkin Musulmi ta Aiyana Gobe Lahadi a Matsayin Ranar 1 Ga Watan Zulqi’ida na Shekarar 1447

Daga Bashir Gasau.

 

Fadar Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta aiyana gobe Lahadi a matsayin ranar 1 ga watan Zulqi’ida na shekarar 1447, bayan hijira.

 

Sarkin Musulmin ya sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin harkokin addinin musulunci na fadar, Farfesa Sambo wali Junaidu (Wazirin Sokoto), ya sanyawa hannu kuma aka raba wa manema labarai a jihar Sokoto.

 

Hotuna: Babbar Jojin Kano ta Rantsar da Sabbin Alƙalan Kotunan Shari’ar Musulunci Guda 30

 

A cewar Wazirin Sokoto, “A ranar Jumu’a 17 ga watan Afrilun shekarar 2026, bamu karbi wani rahoton ganin jinjirin watan Zulqi’ida ba, adan haka yau Asabar ta kasance 30 ga watan Shawwal”.

 

A ƙarshe sanarwar ta ce gobe Lahadi, 19 ga watan Afrilun shekarar 2026, ita ce ranar 1 ga watan Zulqi’ida na shekarar 1447 bayan hijira.

 

Hudubar Jumu’a: Komawa ga Allah ne Mafitar Al’umma – Imam Hussaini Muhammad

The post Fadar Sarkin Musulmi ta Aiyana Gobe Lahadi a Matsayin Ranar 1 Ga Watan Zulqi’ida na Shekarar 1447 appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow