Budaddiyar Wasika ga Gwamnatin Kano Kan Burtalai da Filayen Kiwo – MACBAN Kano

Daga Bashir Gasau.   Shugaban Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association (MACBAN) na kasa reshen jihar Kano, Ambasada Abdullahi Bakoji Adamu (Rtd.), ya aikawa Gwamnatin jihar Budaddiyar Wasika kan Burtalai da Filayen Kiwo.   Bakoji wanda tsohon Soja ne kuma mai sharhi da nazari ne kan harkokin tsaro a Najeriya, ya aika […] The post Budaddiyar Wasika ga Gwamnatin Kano Kan Burtalai da Filayen Kiwo – MACBAN Kano appeared first on GTR .

Budaddiyar Wasika ga Gwamnatin Kano Kan Burtalai da Filayen Kiwo – MACBAN Kano


















Daga Bashir Gasau.

 

Shugaban Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association (MACBAN) na kasa reshen jihar Kano, Ambasada Abdullahi Bakoji Adamu (Rtd.), ya aikawa Gwamnatin jihar Budaddiyar Wasika kan Burtalai da Filayen Kiwo.

 

Bakoji wanda tsohon Soja ne kuma mai sharhi da nazari ne kan harkokin tsaro a Najeriya, ya aika wasikar ne ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ta kasance kamar haka:

 

Tattaunawa da ‘Yan Tagwaye Bayan Kammala Taronsu na Shekara-shekara

 

“MUTUNTA DOKAR ZARTARWA TA GWAMNATIN JIHAR KANO KAN BURTALAI DA FILAYEN KIWO

 

Ni, Amb. Capt. Abdullahi Bakoji Adamu (Mai Ritaya), Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), Reshen Jihar Kano, kuma mai sharhi da nazari kan harkokin tsaro a Najeriya, a madadin ɗaukacin mambobin ƙungiyar, ina sake tunatar da al’ummar Jihar Kano game da muhimmancin mutunta Dokar Zartarwa (Executive Order) da Gwamnatin Jihar Kano ta fitar wadda ta haramta sayarwa, rabawa ko mallakar burtalai da filayen kiwo na gwamnati ba tare da bin tanadin doka ba.

 

Muna kira ga manoma, makiyaya, masu sarautun gargajiya, shugabannin al’umma, jami’an ƙananan hukumomi da duk masu ruwa da tsaki da su mutunta wannan doka tare da gujewa duk wani mataki da zai saɓa da ita. Wannan doka an samar da ita ne domin kare muradun al’umma, tabbatar da zaman lafiya da kuma hana rikice-rikicen da ka iya tasowa sakamakon mamaye ko sayar da filayen kiwo ba bisa ƙa’ida ba.

 

Hotuna: Gwamnan Zamfara ya Karɓi Lambar Yabo ta Zik Pan-African a Ƙasar Ghana

 

Muna sanar da jama’a cewa mun riga mun tattauna da hukumomin da Gwamnatin Jihar Kano ta ɗora wa alhakin aiwatar da wannan Dokar Zartarwa. Saboda haka, duk wanda aka samu da karya dokar, ko ta hanyar saye, sayarwa, rabawa, ko mamaye irin waɗannan filaye, za a miƙa shi ga hukumomin da abin ya shafa domin ɗaukar matakin doka ba tare da nuna bambanci ba.

 

A matsayina na mai nazari kan harkokin tsaro, ina ganin rashin bin wannan doka na iya haifar da manyan barazana ga tsaron jihar, ciki har da:

 

– Ƙaruwar rikice-rikicen manoma da makiyaya.

 

– Mamayar filayen gwamnati ba bisa ƙa’ida ba da haddasa rikice-rikicen mallakar ƙasa.

– Barazana ga zaman lafiya da tsaro a matakin ƙauyuka da ƙananan hukumomi.

 

– Ƙara yawan shari’o’i, tashin hankali da ɗaukar doka a hannu.

 

– Hana gwamnati aiwatar da manufofinta na bunƙasa harkar kiwo da noma cikin tsari.

 

Tsaffin Daliban GATC Gombe Sun Sami Sabbin Mukamai da Ƙarin Girma a Matakan Gwamnatin Najeriya

 

Saboda haka, muna roƙon kowa da kowa da ya bi doka, ya mutunta umarnin Gwamnatin Jihar Kano, kuma ya guji duk wani abu da zai iya jefa al’umma cikin rikici ko rashin zaman lafiya.

 

Muna tabbatar wa gwamnati cikakken goyon bayan Ƙungiyar Miyetti Allah ta Jihar Kano wajen wayar da kan al’umma da kuma haɗin gwiwa da hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da bin doka.

 

Idan kunne ya ji, jiki ya tsira.

Amb. Capt. Abdullahi Bakoji Adamu (Rtd.)

Shugaban, Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), Jihar Kano

Mai Sharhi da Nazari kan Harkokin Tsaro a Najeriya”.

 

Sarkin Malamai ya yi wa ‘Yan Siyasa da Makafin Mabiyansu Wankin Babban Bargo

The post Budaddiyar Wasika ga Gwamnatin Kano Kan Burtalai da Filayen Kiwo – MACBAN Kano appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow