Buɗaɗɗiyar Wasiƙa ga Gwamnatin Kano – Jagorancin Mutane Masu Buƙata ta Musamman (PWDs)

Daga Tasiu Salisu Abdu.   Daya daga cikin Jagororin masu buƙata ta musamman na jihar Kano, Ali Miko Muhammad Dangwauro (Deaf), ya aika buɗaɗɗiyar Wasiƙa ga gwamnatin Kano.   Ali Dangwauro, ya aika buɗaɗɗiyar Wasiƙar ne ta cikin wani rubutaccen saƙo da ya aikowa GTR Hausa kwafi, inda ta kasance kamar haka:   Babu Wani […] The post Buɗaɗɗiyar Wasiƙa ga Gwamnatin Kano – Jagorancin Mutane Masu Buƙata ta Musamman (PWDs) appeared first on GTR .

Buɗaɗɗiyar Wasiƙa ga Gwamnatin Kano – Jagorancin Mutane Masu Buƙata ta Musamman (PWDs)

Daga Tasiu Salisu Abdu.

 

Daya daga cikin Jagororin masu buƙata ta musamman na jihar Kano, Ali Miko Muhammad Dangwauro (Deaf), ya aika buɗaɗɗiyar Wasiƙa ga gwamnatin Kano.

 

Ali Dangwauro, ya aika buɗaɗɗiyar Wasiƙar ne ta cikin wani rubutaccen saƙo da ya aikowa GTR Hausa kwafi, inda ta kasance kamar haka:

 

Babu Wani Zaman Sulhu da Muka Nema da Amurka – Iran

 

“Zuwa ga Gwamnatin Jihar Kano.

 

Assalamu Alaikum Warahmatullah. Ina miƙa wannan wasiƙa ne cikin girmamawa da fatan alheri ga Gwamnatin Jihar Kano, tare da nuna muhimmiyar buƙata da ta shafi rayuwa da makomar Mutane Masu Buƙata ta Musamman wato Persons With Disabilities (PWDs) a jiharmu.

 

Maganar gaskiya ita ce, a siyasance da gwamnatance, duk wata harka da ta shafi bangaren PWDs ya kamata a rika nada shugabanni daga cikinmu. Wannan ba wata buƙata ta son rai ba ce, illa dai hakki ne na adalci, wakilci da fahimta ta gaskiya.

 

Zaben Najeriya ba Zai Zama Mai Cikakken Inganci ba – Shugaban INEC

 

Abin takaici ne a ce ana dora jagorancinmu a hannun mutanen da ba su da wata larurar nakasa a jikinsu. Duk da cewa muna girmama kowa, amma babu wanda zai fi mu fahimtar ƙalubalen da muke fuskanta a rayuwa. Wanda bai rayu da nakasa ba, ba zai iya jin zafin da take haifarwa ko fahimtar bukatun da take tattare da su kamar yadda mu muke ji ba.

 

Saboda haka, muna kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta tabbatar cewa, duk mukaman da suka shafi harkokin nakasa kamar S.A., SSA, Advisers, Shugabanni da Mambobin Hukumar Masu Nakasa, da a rika zabo su daga cikin PWDs.

 

Alkawarin Allah ne ke Shirin Cika Akan Amurka da Isra’ila Shiyasa Suke ta Shure-Shure – Abdulkarimu Daiyabu

 

Shugabannin Makarantun Kurame da Bebaye da sauran makarantun Special Schools su kasance daga cikin waɗanda suka kware kuma suke rayuwa da irin wannan nakasa.

 

Masu kula da ilimi a ɓangaren masu buƙata ta musamman (Coordinator Special Education) a Ma’aikatar Ilimi ta Jihar ya kasance mutum mai cikakkiyar ƙwarewa da gogewa a fannin.

 

A matakai daban-daban na Gwamnati (Jiha da Ƙananan Hukumomi), a rika bai wa PWDs dama su jagoranci harkokin da suka shafe su kai tsaye.

 

Tafsirin Alqur’ani me Girma Daga Masallacin Mopol 52 Kano (Goma Sha Biyu ga Ramadan)

 

Wani abin damuwa shi ne yadda wasu malamai a ɓangaren Special Education ba su da isasshiyar kwarewa musamman a SIGN LANGUAGE da FINGER SPELLING ga Kurame, amma duk da haka ake dorawa kan mukamai. Wannan yana rage ingancin ilimi da ci gaban dalibai masu nakasa wanda ya kamata a sake duba lamarin cikin gaggawa.

 

Muna da yakinin cewa Gwamnatin Kano na da burin gina al’umma mai adalci da hadin kai. Amma ba za a kai ga al’umma mai daidaito ba muddin waɗanda abin ya shafa ba su cikin jagoranci.

 

Nakasa ba ta jiki ba ce kawai domin tana cikin zuciya da tunani. Idan aka ba da dama, aka hada kai, aka girmama hakki, za a ga cewa akwai ƙwarewa da baiwa a cikin abin da wasu ke kira nakasa.

 

Burin Amurka ba Zai Taba Cika ba Duk da ta yi Nasarar Raba Kan Ƙasashen Musulmi – SEDSAC

 

Ni a matsayina na Kurma, ina ganin “Ability” a cikin “Disability”. Don haka ina sake jaddada bukatarmu ta a ba mu dama, a karfafa mu, kuma a shigar da mu cikin tsarin yanke shawara da jagoranci.

 

Muna roƙon Gwamnatin Jihar Kano da ta ɗauki wannan kira da muhimmanci domin tabbatar da adalci, wakilci da daidaito ga dukkanin Mutane Masu Buƙata ta Musamman a jiharmu.

 

Allah Ya taimaki Kano, Ya kuma ba mu shugabanci mai adalci

Na gode.

Ali Miko Muhammad Dangwauro (Deaf) @#MikoDanAbdallah”.

 

Gaskiyar Lamari Kan Yaƙin da ke Faruwa Tsakanin Iran da Kuma Amurka da Isra’ila – Farfesa Sani Umar R/Lemo

The post Buɗaɗɗiyar Wasiƙa ga Gwamnatin Kano – Jagorancin Mutane Masu Buƙata ta Musamman (PWDs) appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow