Babbar Kotun Taraiya ta Gargaɗi ACP Babagana na Zone One Kano, Kan Ƙin Bin Umarnin ta

Daga Bashir Gasau.   Babbar Kotun Tarayya dake Kano ta gargaɗi jami’in rundunar ‘yan sanda na Zone One da ke kano, ACP Babagana, kan zargin kin bin umarnin Kotu tare da jaddada umarninta na ci-gaba da kiyaye gida me lamba 17 a layin UDB dake unguwar Hotoro.     Hukuncin ya biyo bayan karar da […] The post Babbar Kotun Taraiya ta Gargaɗi ACP Babagana na Zone One Kano, Kan Ƙin Bin Umarnin ta appeared first on GTR .

Babbar Kotun Taraiya ta Gargaɗi ACP Babagana na Zone One Kano, Kan Ƙin Bin Umarnin ta












Daga Bashir Gasau.

 

Babbar Kotun Tarayya dake Kano ta gargaɗi jami’in rundunar ‘yan sanda na Zone One da ke kano, ACP Babagana, kan zargin kin bin umarnin Kotu tare da jaddada umarninta na ci-gaba da kiyaye gida me lamba 17 a layin UDB dake unguwar Hotoro.

 

Babbar Kotun Taraiya ta Gargaɗi ACP Babagana na Zone One Kano, Kan Ƙin Bin Umarnin ta

 

Hukuncin ya biyo bayan karar da Alkasim Musa da Mahaboob Mohammed Radman, suka shigar a gaban kotun kan takaddamar mallakar filin, ta hannun Lauyansu, Barista Bashir Yusif Muhammad, inda suka zargi ACP Babagana da raina kotu, ta hanyar tura jami’ai wurin da ake takaddama akai, duk kuwa da umarnin kotu na cewa kowa ya dakata.

 

Hotuna: Anyi Jana’izar Mutanen da ‘Yan Bindiga Suka Hallaka a Yayin Garkuwa da Shugaban Ƙaramar Hukumar Bungudu ta Zamfara

 

Mai shari’a, Simon A. Amobeda, ya ce kotun ta gamsu da hujjojin da aka gabatar cewa, ACP Babagana, ya yi watsi da umarnin kotun duk da cewa an ba shi takardar gargadi (Form 48), baya ga zargin shi da ci-gaba da aikata abubuwan da ka iya haddasa tashin hankali da kuma kawo cikas ga gudanar da adalci.

 

Babbar Kotun Taraiya ta Gargaɗi ACP Babagana na Zone One Kano, Kan Ƙin Bin Umarnin ta

 

Haka kuma kotun ta umarci babban Sufeton na Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, da ya tabbatar an aiwatar da umarnin kotun, tare da daukar matakin ladabtarwa kan ACP Babagana, harma ta ce duk wanda aka samu a wurin ba tare da izini ba yayin da umarnin ke aiki, zai iya fuskantar tsarewa har sai an kammala shari’ar.

 

Satar Shugaban Karamar Hukuma a Jihar Zamfara ba Abin Mamaki Bane – Rundunar Adalci

 

Haka kuma Kotun ta umarci Gwamnatin Jihar Kano da Kwamishinan Filaye su dauki matakan kare filin, sannan kuma hukumar tsaro ta Civil Defence ta karbi ragamar kula da wurin, tare da tabbatar da dawo da duk kayayyakin da aka debe daga gidan.

 

 

Duk Al’ummar da ta Fifita Kudi Akan Mutunci, Toh ta Kauce Hanyar Gaskiya – Ambasada Gashash

The post Babbar Kotun Taraiya ta Gargaɗi ACP Babagana na Zone One Kano, Kan Ƙin Bin Umarnin ta appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow