Al’ummar Gobirawa Sun Buƙaci Aliyu Madakin Gini ya Ƙarasa Aikin Titin da Sanata Barau ya Fara

Daga Bashir Gasau.   Al’ummar unguwar Gobirawa ta ƙaramar hukumar Dala da ke jihar Kano, sun buƙaci wakilinsu a majalisar wakilan Najeriya, Honarabul Aliyu Sani Madakin Gini, ya ƙarasa aikin titin da Sanatan Kano ta Arewa, Barau Jibrin, ya fara.   Mazauna yankin sun bayyana cewa rashin kammala aikin titin wanda ya tashi daga Kurna […] The post Al’ummar Gobirawa Sun Buƙaci Aliyu Madakin Gini ya Ƙarasa Aikin Titin da Sanata Barau ya Fara appeared first on GTR .

Al’ummar Gobirawa Sun Buƙaci Aliyu Madakin Gini ya Ƙarasa Aikin Titin da Sanata Barau ya Fara

Daga Bashir Gasau.

 

Al’ummar unguwar Gobirawa ta ƙaramar hukumar Dala da ke jihar Kano, sun buƙaci wakilinsu a majalisar wakilan Najeriya, Honarabul Aliyu Sani Madakin Gini, ya ƙarasa aikin titin da Sanatan Kano ta Arewa, Barau Jibrin, ya fara.

 

Mazauna yankin sun bayyana cewa rashin kammala aikin titin wanda ya tashi daga Kurna Farin Bene zuwa Babban Layi, yana ci-gaba da jefa al’umma cikin wahalhalu musamman a lokacin damina.

 

Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) na Duba Yiwuwar Ƙara Mafi Ƙarancin Albashi Zuwa N100,000

 

A cewarsu, “Titin na da matuƙar muhimmanci ga harkokin sufuri da kasuwanci, kasancewar ya haɗa unguwanni da dama tare da sauƙaƙa zirga-zirgar al’umma a yankin Gobirawa da kewaye”.

 

Adan haka suka roki wakilin nasu da ya kawo musu ɗauki ganin irin aiyukan alherin da yake gudanarwa a mazaɓarsa, musamman yadda ya shimfiɗa titi a yankin Kurna ‘Yan Ganda, aikin da suka bayyana a matsayin wanda ya kawo sauƙi da ci-gaban mazauna yankin.

 

A ƙarshe sun yi fatan ɗan majalisar zai duba rokon nasu ta hanyar kammala aikin titin, domin inganta rayuwar jama’a da bunƙasa ci-gaban yankin.

 

Cire Tallafin Mai ya Ceci Najeriya Daga Durƙushewar Tattalin Arziƙi – Tinubu

The post Al’ummar Gobirawa Sun Buƙaci Aliyu Madakin Gini ya Ƙarasa Aikin Titin da Sanata Barau ya Fara appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow