Akwai Buƙatar Samarwa Ma’aikatan Najeriya Ƙarin Alawus Saboda Tsadar Rayuwa

Daga Bashir Gasau.   Dan Gwagwarmayar nan, Kwamared Jabir A. Bichi, ya shawarci Gwamnatin Najeriya da ta jihohi kan su samarwa Ma’aikatansu ƙarin Alawus domin rage musu tsadar rayuwa   Jabir Bichi ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya ce ma’aikaci shi ne ginshiƙin tafiyar gwamnati, […] The post Akwai Buƙatar Samarwa Ma’aikatan Najeriya Ƙarin Alawus Saboda Tsadar Rayuwa appeared first on GTR .

Akwai Buƙatar Samarwa Ma’aikatan Najeriya Ƙarin Alawus Saboda Tsadar Rayuwa

Daga Bashir Gasau.

 

Dan Gwagwarmayar nan, Kwamared Jabir A. Bichi, ya shawarci Gwamnatin Najeriya da ta jihohi kan su samarwa Ma’aikatansu ƙarin Alawus domin rage musu tsadar rayuwa

 

Jabir Bichi ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya ce ma’aikaci shi ne ginshiƙin tafiyar gwamnati, kuma duk gwamnatin da ta baiwa ma’aikatanta kulawa da walwala to lallai za ta sami ingantaccen aiki da ci-gaba mai ɗorewa.

 

AUFCDN ta sha Alwashin Bunkasa Harkokin Noma da Kiwo a Fadin Najeriya

 

A cewarsa, ina kira ga gwamnonin jahohin Najeriya da su ƙara duba hanyoyin da za su inganta rayuwar ma’aikata a dukkan matakai, ta hanyar samar musu da alawus na musamman a tsakiyar kowanne wata, domin rage musu raɗaɗin matsin tattalin arziƙi da kuma ƙara musu ƙwarin guiwa wajen gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da aminci”.

 

A ƙarshe ya ce hakan zai taimaka wajen rage damuwa ga ma’aikata, ƙarfafa musu guiwa, da kuma bunƙasa kyakkyawar alaƙa tsakanin gwamnati da ma’aikata, musamman a wannan lokaci da al’umma ke fama da matsin tattalin arziƙi a sakamakon tsadar rayuwa.

 

Akwai Buƙatar Shugaba Tinubu ya Waiwayi Ƙudirin Tabbatar da Ƙungiyar ‘Yan Sintiri ta Najeriya – Godwin Ayinda

The post Akwai Buƙatar Samarwa Ma’aikatan Najeriya Ƙarin Alawus Saboda Tsadar Rayuwa appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow