Akpabio ya Bude Makon Budaddiyar Majalisar Dokoki ta Ƙasa, ya Buƙaci Kara Gaskiya da Riƙon Amana

Daga Bashir Gasau.   A jiya Talata ne, Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya buɗe bikin Makon Buɗaɗɗiyar Majalisar Dokoki ta Ƙasa, a zauren Majalisar Wakilai da ke Abuja.   An ƙaddamar da shirin ne domin nuna ƙudurin majalisar na gudanar da aiyukanta cikin gaskiya da riƙon amana, da kuma ƙarfafa amincewar jama’a […] The post Akpabio ya Bude Makon Budaddiyar Majalisar Dokoki ta Ƙasa, ya Buƙaci Kara Gaskiya da Riƙon Amana appeared first on GTR .

Akpabio ya Bude Makon Budaddiyar Majalisar Dokoki ta Ƙasa, ya Buƙaci Kara Gaskiya da Riƙon Amana












Daga Bashir Gasau.

 

A jiya Talata ne, Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya buɗe bikin Makon Buɗaɗɗiyar Majalisar Dokoki ta Ƙasa, a zauren Majalisar Wakilai da ke Abuja.

 

An ƙaddamar da shirin ne domin nuna ƙudurin majalisar na gudanar da aiyukanta cikin gaskiya da riƙon amana, da kuma ƙarfafa amincewar jama’a tare da bai wa masu ruwa da tsaki damar shiga cikin aiyukan Majalisa ta goma.

 

Da yake jawabi yayin buɗe taron, Sanata Akpabio ya ce majalisar ta kasance mallakin al’ummar Najeriya baki ɗaya, ba na waɗanda aka zaɓa kawai ba.

 

Jam’iyyu Uku Sun Makara Yayin da INEC ta Rufe Karbar Sunayen ‘Yan Takara

 

A cewar Akpabio, “Mun taru a yau ne saboda wani muhimmin al’amari da ya fi kowacce daga cikin majalisun biyu girma. Majalisar dokoki ta kasance mallakin miliyoyin ‘yan Najeriya waɗanda ƙuri’unsu da fatansu suka haifar da ita.”

 

Ya ƙara da cewa ba a kafa majalisa domin ware jama’a daga harkokin gwamnati ba, sai dai domin su kasance cikin tafiyar demokraɗiyya.

 

“Dimokuraɗiyya tana bunƙasa ne idan ‘yan ƙasa suna da cikakken bayani kuma suna taka rawa a cikin harkokin ƙasa. Wannan Makon Buɗaɗɗiyar Majalisa wata dama ce ga ‘yan Najeriya su fahimci yadda majalisa ke aiki fiye da abin da suke gani a kanun labarai,” in ji shi.

 

Majalisar Dokokin Kano ta Soke Dokar da ta Kafa Hukumar KNUPDA

 

Akpabio ya ce tarihi ya nuna cewa ƙasashe masu ci gaba ba sa dogaro da ɓangaren zartarwa ko na shari’a kaɗai, illa suna samun ƙarfi ne ta hanyar majalisun dokoki da ke sauraron mabambantan ra’ayoyi tare da ba kowane ɗan ƙasa damar samun wakilci.

 

Ya kuma ce manufar buɗe ƙofofin majalisar ba wai bai wa jama’a damar kallon zaman majalisa kawai ba ne, amma tabbatar da cewa babu wata al’umma ko yanki da aka bari a baya wajen samun wakilci.

 

Akpabio ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da mu’amala da majalisar tare da bayyana ra’ayoyinsu.

 

Sarkin Musulmin Najeriya ya Aiyana Gobe Alhamis a Matsayin Ranar 1 ga Watan Safar na Shekarar 1448

 

“Muna gayyatar ‘yan Najeriya ba kawai su kalli ayyukanmu ba, har ma su tattauna da mu. Su yaba idan mun yi daidai, su kuma yi mana gyara idan suna ganin akwai inda za mu inganta. Majalisar da ke sauraron jama’a tana ƙara hikima, dimokuraɗiyya kuma tana ƙara ƙarfi,” in ji shi.

 

A nasa jawabin, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce an kafa shirin Makon Buɗaɗɗiyar Majalisa ne bisa imanin cewa majalisar da ke buɗe ƙofofinta tare da sauraron jama’a ita ce ke samun amincewar al’umma tare da ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyya.

 

Ana sa ran taron na kwanaki uku zai haɗa manyan tarurruka da tattaunawa da suka shafi jama’a, domin ƙara kusantar da ‘yan ƙasa, ɓangaren masu zaman kansu da masu tsara manufofin gwamnati.

 

An Kama Mutumin da Ake Zargi da Kirkirar Hukumar Bogi (PFIPC) a Najeriya

The post Akpabio ya Bude Makon Budaddiyar Majalisar Dokoki ta Ƙasa, ya Buƙaci Kara Gaskiya da Riƙon Amana appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow