Zamu Zaƙulo Dukkan Mutanen da Suka Rasa Wani Sashe na Jikinsu Domin Kula Dasu a Fadin Najeriya – HAF’D

Daga Kallamu Galadima Dambo.   Gidauniyar tallafawa masu bukata ta musamman a Najeriya wato Help the Amputee Foundation (HAF’D), ta sha alwashin yin aiki da kungiyoyin mata domin zaƙulo wadanda suka rasa wani sashe na jikinsu a fadin Najeriya, domin basu tallafin kula da lafiyarsu.   Shugaban Gidauniyar na Najeriya, Ambasada Dakta Tizhe Joseph Kwaji, […] The post Zamu Zaƙulo Dukkan Mutanen da Suka Rasa Wani Sashe na Jikinsu Domin Kula Dasu a Fadin Najeriya – HAF’D appeared first on GTR .

Zamu Zaƙulo Dukkan Mutanen da Suka Rasa Wani Sashe na Jikinsu Domin Kula Dasu a Fadin Najeriya – HAF’D

Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

Gidauniyar tallafawa masu bukata ta musamman a Najeriya wato Help the Amputee Foundation (HAF’D), ta sha alwashin yin aiki da kungiyoyin mata domin zaƙulo wadanda suka rasa wani sashe na jikinsu a fadin Najeriya, domin basu tallafin kula da lafiyarsu.

 

Shugaban Gidauniyar na Najeriya, Ambasada Dakta Tizhe Joseph Kwaji, ne ya sanar da hakan a lokacin da yake karɓar lambar yabo, daga gamayyar ƙungiyoyin matan Najeriya masu fafutukar wanzar da zaman lafiya da samar da shugabanci na Nagari da kuma kungiyar dalibai mata zalla a Ofishinsa da ke Sakatariyar kasa a Babban Birnin Tarayya Abuja.

 

Gwamnatin Kano za ta Ƙaddamar da Shirin Yaki da Cutar Murar Tsuntsaye

 

A cewar Dakta Tizhe, “Manufar gidauniyarmu ita ce taimakawa masu ƙaramin ƙarfi da suka rasa wasu sassa na jikinsu kamar Hannu, Ƙafa, Kunne, Ido dama dukkan wata Tawaya a sakamakon harin ta’addanci, hatsarin mota ko gobara da dai sauransu”.

 

Zamu Zaƙulo Dukkan Mutanen da Suka Rasa Wani Sashe na Jikinsu Domin Kula Dasu a Fadin Najeriya - HAF’D

 

Harma ya ce ko a shekarar 2025 da ta gabata, gidauniyar ta tallafawa wadanda suka rasa wasu sassa na jikinsu, inda suka sanya sama da yara 150 a makaranta bayan da ricikin ta’addanci ya ritsa da su a jihar Yobe dake yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

 

Muhadara: Lakcar Iyaye Mata Akan Tarbiyya (Tara ga Ramadan) – CSP Salihu Idris (Alburhan)

 

Daga bisani ya baiyana matuƙar farin cikinsa bisa yadda ƙungiyoyin suka zaƙulo shi domin karramashi da lambobin yabo, a matsayin wanda ya shahara ta fuskar hidimtawa al’umma, adon haka ya sha alwashin yin aiki dasu don rubanya kokarinsa.

 

Zamu Zaƙulo Dukkan Mutanen da Suka Rasa Wani Sashe na Jikinsu Domin Kula Dasu a Fadin Najeriya - HAF’D

 

A nata jawabin, Shugabar gamayyar ƙungiyoyin matan Najeriya dake fafutikar wanzar da zaman lafiya da samar da shugabanci na Nagari reshen jihar katsina, Khalisa Abdullahi, ta ce sun karramashi ne a sakamakon yadda ya shahara wajen hidimtawa al’umma, wanda kuma aikin kungiyarsu na kamanceceniya da aiyukan gidauniyar HAF’D, la’akari da yadda suke maida hankali wajen samar da kayan tsaftar jiki ga takwarorinsu mata da koyar da sana’oi ga wadanda rikicin ‘yan ta’adda ya rutsa da su.

 

Hotuna: Yadda IGP Tunji Disu ke Karbar Faretin Ban-girma

 

Itama shugabar Ƙungiyar ɗalibai mata zalla reshen jihar kaduna, Khadija Ibrahim, ta ce Kungiyarsu ta mayar da hankali akan mata marasa galihu da marayu ta fuskar tallafa masu a harkokin kiwon lafiya da kuma ilimi.

 

A ƙarshe Dakta Joseph kwaji, ya nemi hadin-kai da goyon baya, musamma daga gwamnatin tarayya dama na jihohin da hare haren ‘yan ta’adda yayi ƙamari, domin ganin an magance dukkan matsalolin da irin waɗannan al’ummomi ke fuskanta.

 

Hotuna: Hukumar Zakka ta Sokoto na Ci-gaba da Rabon Tallafin da Dan Iyan Jarma ya Bayar

The post Zamu Zaƙulo Dukkan Mutanen da Suka Rasa Wani Sashe na Jikinsu Domin Kula Dasu a Fadin Najeriya – HAF’D appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow