‘Yan Sandan Jigawa Sun Kama Wadanda Ake Zargi da Aikata Damfara ta Hanyoyi Daban-daban

Daga Bashir Gasau.   Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta sami nasarar kama wasu mutane da take zargi da aikata damfara ta hanyoyi daban-daban kuma a mabanbantan wurare.   Kakakin rundunar na jihar Jigawa, SP Shiisu Lawan Adam, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya […] The post ‘Yan Sandan Jigawa Sun Kama Wadanda Ake Zargi da Aikata Damfara ta Hanyoyi Daban-daban appeared first on GTR .

‘Yan Sandan Jigawa Sun Kama Wadanda Ake Zargi da Aikata Damfara ta Hanyoyi Daban-daban












Daga Bashir Gasau.

 

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta sami nasarar kama wasu mutane da take zargi da aikata damfara ta hanyoyi daban-daban kuma a mabanbantan wurare.

 

Kakakin rundunar na jihar Jigawa, SP Shiisu Lawan Adam, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya ce sun ƙwato Katunan cirar Kudi (ATM) guda 36, bindiga ƙirar gida da babur da aka sace.

 

Garus Gololo ya yi wa Ministan Shari’a Shagube Kan Shari’ar Omowole Sowore

 

Da farko an kama Hafsatu Usman daga Ƙaramar Hukumar Dutse, wadda ake zargi da cin amana ta hanyar guduwa da Naira milyan 10.5, a inda aka kamo ta a jihar Gombe.

 

Hakazalika, jami’an sun gano wata ƙungiyar ‘yan damfara da suka yaudari Matar wani Ado Muhammad daga garin Jobi na Ƙaramar Hukumar Maigatari, ta hanyar WhatsApp, wadda take zaune a kasar Saudiyya, inda suka yi mata ƙaryar cewa suna iya yin tsafin samun kuɗi, mafari kenan da suka damfare ta Naira milyan 12,923,000.

 

Gwamnan Kaduna ya Zaɓi Jerry Adams a Matsayin Mataimakinsa a zaɓen 2027

 

Bayan zurfafa bincike, jami’an suka gano lambar WhatsApp da asusun bankunan da aka yi amfani da su wajen aikata laifin, lamarin da ya kai ga kama Ismail Adam Abdullahi, mai shekaru 21, mazaunin Hayin Ojo, unguwar Bakin Dogo na Zariyan Jihar Kaduna.

 

Haka Zalika an kama Kassim Ali, mai shekaru 27, mazaunin unguwar Gyadi-Gyadi, Ƙaramar Hukumar Tarauni ta Jihar Kano, bayan samun kiran gaggawa daga Bankin Access Bank, kan zargin ya damfari wata kwastoma ta hanyar sauya mata katin ATM sannan ya cire kuɗi daga asusunta ba bisa ƙa’ida ba, harma aka sami katunan ATM guda 36 na bankuna daban-daban a hannunsa.

 

AUFCDN da IMP Sun Kulla Yarjejeniyar Zamanantar da Sana’ar Fawa a Najeriya

 

A karshe sanarwar ta ce ta sami nasarar ceto wani mutum da bata gari suka buge shi suka gudu da Baburinsa akan titin Sabuwar Gwaram zuwa Kila, inda daga bisani wadanda ake zargin suka yasar da baburin tare da bindigar revolver ɗauke da harsasai guda huɗu masu rai da kuma kwanson harsasai biyu da aka harba, bayan jami’an ’yan sanda sun bi sawunsu.

 

Mukhtasar Khalil (Darasi na 3): Bayanin Lokacin Sallar Shahid Ko Hadir – CSP Salihu Idris (Alburhan)

The post ‘Yan Sandan Jigawa Sun Kama Wadanda Ake Zargi da Aikata Damfara ta Hanyoyi Daban-daban appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow