Tinubu ya Kara wa Sojojin Najeriya Albashi

Daga Bashir Gasau.   Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya karawa Sojojin kasar albashi, daga kashi 30 zuwa 80 cikin 100, inda ake sa ran kusan ma’aikata 250,000 za su amfana da sabon tsarin albashin.   Mashawarcin Shugaban Ƙasar kan yaɗa Labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa […] The post Tinubu ya Kara wa Sojojin Najeriya Albashi appeared first on GTR .

Tinubu ya Kara wa Sojojin Najeriya Albashi












Daga Bashir Gasau.

 

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya karawa Sojojin kasar albashi, daga kashi 30 zuwa 80 cikin 100, inda ake sa ran kusan ma’aikata 250,000 za su amfana da sabon tsarin albashin.

 

Mashawarcin Shugaban Ƙasar kan yaɗa Labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata, inda ya ce karin albashin zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumbar shekarar 2026.

 

‘Yan Siyasar Kano Duk Marowata ne – Dakta Sunusi Balarabe

 

A cewarsa, “A sabon tsarin, jami’an da suke sama da matsayin kanar, ciki har da Birgediya-Janar, Manjo-Janar, Laftanar-Janar da Janar, za su samu ƙarin albashi na kashi 30 cikin 100”.

 

Haka kuma Jami’an da suke daga matsayin kanar zuwa warrant officer za su samu ƙarin kashi 50 cikin 100, yayin da waɗanda suke daga matsayin soja mai zaman kansa (Private) zuwa Staff Sergeant za su samu ƙarin kashi 80 cikin 100.

 

Sarkin Hadejia ya Naɗa Limamai Bakwai da Na’ibai Biyar

 

Ana sa ran sabon tsarin albashin zai ƙara yawan kuɗin da ake kashewa duk shekara wajen biyan albashin jami’an Sojin Najeriya daga Naira Bilyan 660 zuwa Naira Bilyan 924.

 

A karshe sanarwar ta ce wannan mataki wani ɓangare ne na ƙudirin gwamnatin Tinubu na inganta jin daɗin jami’an tsaro, waɗanda ke taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma ta’addanci a faɗin ƙasar.

 

Karin Hasken Jami’ar Bayero ta Kano Kan Haramta Cajin Babura da Motoci Masu Amfani da Lantarki

The post Tinubu ya Kara wa Sojojin Najeriya Albashi appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow