Sabon Rikicin da ya Kunno Kai a Jam’iyyar NDC, ya Haddasa Canza Wasu ‘Yan Takarar Kwankwaso a Kano

Daga Bashir Gasau.   Jam’iyyar NDC ta sauya sunayen wasu daga cikin ‘yan takarar da bangaren Kwankwasiyya ya gabatar mata a Kano, domin cika yarjejeniyar rabon tikitin takara da aka cimma tsakanin bangaren jam’iyyar da aka tarar da kuma bangaren Kwankwasiyya.   Kadaura24 ta rawaito a wata takarda da shugaban jam’iyyar a Kano, Hon. Hussaini […] The post Sabon Rikicin da ya Kunno Kai a Jam’iyyar NDC, ya Haddasa Canza Wasu ‘Yan Takarar Kwankwaso a Kano appeared first on GTR .

Sabon Rikicin da ya Kunno Kai a Jam’iyyar NDC, ya Haddasa Canza Wasu ‘Yan Takarar Kwankwaso a Kano

Daga Bashir Gasau.

 

Jam’iyyar NDC ta sauya sunayen wasu daga cikin ‘yan takarar da bangaren Kwankwasiyya ya gabatar mata a Kano, domin cika yarjejeniyar rabon tikitin takara da aka cimma tsakanin bangaren jam’iyyar da aka tarar da kuma bangaren Kwankwasiyya.

 

Kadaura24 ta rawaito a wata takarda da shugaban jam’iyyar a Kano, Hon. Hussaini Isah Mairiga, ya sanya wa hannu, wadda aka aikewa jagoran jam’iyyar na kasa, Sanata Seriake Dickson, jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da shugaban NDC na shiyyar Arewa maso Yamma, Alhaji Muhammadu Rabi’u Sabo Bakinzuwo.

 

Dan Takarar Gwamnan Kano ya Shawarci Iyaye su Hana ‘Ya’yansu Gangamin Yakin Neman Zaɓe

 

A cewar takardar, jam’iyyar ta amince da Barista Isma’il Idris Sani a Kumbotso, Nasiru Ali Ahmed a Nassarawa, Kabiru Ishaq Sa’id a Kano Municipal, Barista Ɗayyabu Jamilu Ibrahim a Doguwa da Tudunwada, Muhammad Hamisu Abubakar a Dawakin Tofa, Rimin Gado da Tofa, Ibrahim Bashir Bango a Sumaila da Takai, da kuma Abdulmajid Isa Umar Mairigar fata a Gwale a matsayin ‘yan takarar Majalisar Tarayya.

 

Haka kuma, an samu sauye-sauye a tikitin takarar Majalisar Jiha a kananan hukumomin Dala, Tarauni, Kumbotso, Ungogo da kuma Dawakin Kudu.

 

Jam’iyyar ta bayyana cewa tun a farko akwai yarjejeniya tsakaninta da Kwankwaso cewar za a yi rabon mukaman jam’iyyar da na takara a tsarin kaso 60 bangaren Kwankwasiyya sai kuma jam’iyya za ta ɗauki kaso 40.

 

Bidiyo: GMBNI ta Shiryawa Sheikh Nura Khalid, Addu’oi na Musamman Kan Rashin Lafiyar da Yayi a Saudiyya

 

Sai dai Rahotanni sun nuna cewa babu wata kujera da ɓangaren Kwankwasiyyar ya baiwa bangaren jam’iyya, lamarin da ya kawo saɓani da har ta kai jam’iyyar ta ɗauki matakin ɗaukar kason ta.

 

Wannan ce tasa yan asalin jam’iyyar NDC a jihar Kano suka rubutar takardar koke ga jagoran jam’iyyar na Kasa Seriaki Dickson domin yin duban kan lamarin.

 

Sai dai duk kokarin da jagoran ya yi na ganin ya sasanta rikicin Amma hakan Bai yiwu ba, saboda shi Kwankwaso ya dage kai da fata cewa shi ne yake da ikon jam’iyyar a jihar Kano.

 

Sanarwar ta ce wannan dalili ne y sanya jam’iyyar yin amfani da karfin ikonta na chanza sunan wasu ‘yan Kwankwasiyya a wasu ƙananan hukumomin a Kano ta tsakiya.

 

Bidiyo: Yadda Bikin Nadin Dallatun Baburawan Kano, Alhaji Bulama Isa Danjuma, ya Kasance

 

Da yake mayar da martani kan zargin, Mai magana da yawun kungiyar Kwankwasiyya, Habibu Sale mailemo, ya musanta zargin inda ya ce ba shi da tushe ballanta makoma.

 

A cewar Mailemo, “Ba a hana kowa siyen fom din takara ba, domin jam’iyya ce ke siyar da fom, ba ƙungiyar Kwankwasiyya ba”.

 

A ƙarshe Habib Sale ya jaddada cewa an bai wa duk masu sha’awar tsayawa takara damar shiga tsarin zaɓen fidda gwani, yana mai bayyana zarge-zargen da ake yi a matsayin marasa tushe.

 

Fitaccen Dan Jarida, Alhaji Adamu Ibrahim Getso ya Rasu

The post Sabon Rikicin da ya Kunno Kai a Jam’iyyar NDC, ya Haddasa Canza Wasu ‘Yan Takarar Kwankwaso a Kano appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow