NAPTAN ta Buƙaci ‘Yan Kasuwa da su Zuba Jari a Fannin Noman Tumatur

Daga Usman Hamza, Kano.   Haddadiyar Ƙungiyar manoma Tumatur da sarrafashi ta Najeriya (NAPTAN), ta yi kira ga ‘Yan kasuwa da masu Hannu da shuni da su zuba Jari a fannin noman Tumatur.   Sakatare Janar na Ƙungiyar na Ƙasa, Alhaji Sani Danladi Yadakwari, ne ya buƙaci hakan a yayin zantawar sa da manema labarai […] The post NAPTAN ta Buƙaci ‘Yan Kasuwa da su Zuba Jari a Fannin Noman Tumatur appeared first on GTR .

NAPTAN ta Buƙaci ‘Yan Kasuwa da su Zuba Jari a Fannin Noman Tumatur

Daga Usman Hamza, Kano.

 

Haddadiyar Ƙungiyar manoma Tumatur da sarrafashi ta Najeriya (NAPTAN), ta yi kira ga ‘Yan kasuwa da masu Hannu da shuni da su zuba Jari a fannin noman Tumatur.

 

Sakatare Janar na Ƙungiyar na Ƙasa, Alhaji Sani Danladi Yadakwari, ne ya buƙaci hakan a yayin zantawar sa da manema labarai a ofishinsa dake Kano, inda ya ce noman Tumatur da sarrafashi na samar da kudin shiga me dumbin yawa.

 

Hotuna: Yadda Mata Maniyyata Suka Fara Karɓar Bitar Aikin Hajjin Bana a Jihar Sokoto

 

A cewar Yadakwari, “Noman Tumatur abune me matukar samar da Kuɗin shiga ga al’ummar kasar nan, duba da yadda mutane ke bukatarsa a aiyukansu na yau da kullum ba sai a lokacin sanyi ba”.

 

Adan haka Sakataren, wanda shine Shugaban Ƙungiyar na jihar Kano ya ce shigowar ‘Yan kasuwar zai samar da riba ga Kamfanonin sarrafa Tumatur musamman a lokaci da yake Bozo a kasuwa, wanda itama gwamnati zai bunkasa Kudin shigarta harma da rage matsalolin tsaro a sakamakon samar da aikin yi a lungu da saƙo na ƙasar nan.

 

Amurka da Iran Sun Gaza Ƙulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya a Pakistan

 

A ƙarshe ya yabawa gwamnatin taraiya a bisa samar da shirye-shiryenta na inganta fannin noma musamman na Tumatur, a inda kuma ya kalubalanci gwamnatin Kano kan rashin basu wani tallafi a sha’anin noman Tumatur.

 

Gwamnatin Najeriya ta Fitar da Sunayen Mutane da Ƙungiyoyin da Take Zargin Suna Tallafawa Aiyukan Ta’addanci a Ƙasar

The post NAPTAN ta Buƙaci ‘Yan Kasuwa da su Zuba Jari a Fannin Noman Tumatur appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow