Najeriya da Burtaniya Sun Ƙarfafa Haɗin Guiwa Don Fuskantar Kalubalen Tsaro

Daga Kallamu Galadima Dambo.   Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), ya sake jaddada aniyar kasar na ci-gaba da ƙarfafa haɗin guiwa da Birtaniya domin fuskantar ƙalubalen tsaro da ke ƙara sauyawa a duniya.   Janar Musa ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar Mai bada Shawara kan Tsaron […] The post Najeriya da Burtaniya Sun Ƙarfafa Haɗin Guiwa Don Fuskantar Kalubalen Tsaro appeared first on GTR .

Najeriya da Burtaniya Sun Ƙarfafa Haɗin Guiwa Don Fuskantar Kalubalen Tsaro

Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), ya sake jaddada aniyar kasar na ci-gaba da ƙarfafa haɗin guiwa da Birtaniya domin fuskantar ƙalubalen tsaro da ke ƙara sauyawa a duniya.

 

Janar Musa ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar Mai bada Shawara kan Tsaron Ƙasa na Burtaniya, Jonathan Powell, a Ofishinsa da ke Abuja, a yayin da tawagar ta halarci taron tattaunawar Haɗin Guiwar Tsaro da Tsaron Soja tsakanin ƙasashen biyu a karo na huɗu (SDP4).

 

Najeriya da Majalisar Dinkin Duniya za su Kara Hada Kai Don Kare Hakkin Dan Adam Da Tallafawa Wadanda Rikice-rikice ya Shafa

 

A yayin ganawar, Ministan Tsaron ya jaddada muhimmancin ƙara ƙarfafa alaƙar ƙasashen biyu, musamman a fannonin yaƙi da ta’addanci, musayar bayanan sirri da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin.

 

A cewar Gwabin Musa, “Najeriya na daraja alaƙar tarihi da ta dabarun tsaron da Burtaniya ke da su, wanda kuma haɗin guiwar na ci-gaba da taka muhimmiyar rawa wajen inganta tsaron ƙasar nan”.

 

Cikakken Rahoto Kan Taron Wayar da Kan Malamai Wanda Alkalanci Media ta Shirya

 

Bangarorin biyu sun kuma amince da sake duba yarjejeniyoyin fahimtar juna (MoUs) da ke tsakanin Najeriya da Birtaniya, domin sabunta tsare-tsaren tsaro, faɗaɗa horaswa da ƙara bunƙasa ƙwarewar rundunar sojojin Najeriya.

 

Sanarwar da mai taimaka wa Ministan kan yada labarai, Misis Leah Katung-Babatunde, ta aikowa GTR Hausa ta ce, taron SDP4 na kwanaki biyu ya gudana ne a Ofishin Mai bawa shugaban kasa Shawara kan Tsaro (ONSA) a Abuja, ƙarƙashin jagorancin Mallam Nuhu Ribadu da Jonathan Powell.

 

Gwamnan Kano ya Kafa Kwamitin Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi

The post Najeriya da Burtaniya Sun Ƙarfafa Haɗin Guiwa Don Fuskantar Kalubalen Tsaro appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow