MSSN ta yi Allah-wadai da Cin Zarafin Daliba Musulma a Wajen Jarrabawar UTME a Abuja

Daga Kallamu Galadima Dambo.   Ƙungiyar Dalibai Musulmi ta Najeriya (MSSN), ta yi Allah-wadai da cin Zarafin Daliba Musulma a Wajen Jarrabawar UTME a Abuja.   Shugaban Ƙungiyar na jihohi 19 da Abuja, Ado Garba Yankaji, ne ya yi Allah-wadan ta cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce bincikensu ya gano cewa an […] The post MSSN ta yi Allah-wadai da Cin Zarafin Daliba Musulma a Wajen Jarrabawar UTME a Abuja appeared first on GTR .

MSSN ta yi Allah-wadai da Cin Zarafin Daliba Musulma a Wajen Jarrabawar UTME a Abuja

Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

Ƙungiyar Dalibai Musulmi ta Najeriya (MSSN), ta yi Allah-wadai da cin Zarafin Daliba Musulma a Wajen Jarrabawar UTME a Abuja.

 

Shugaban Ƙungiyar na jihohi 19 da Abuja, Ado Garba Yankaji, ne ya yi Allah-wadan ta cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce bincikensu ya gano cewa an wulakanta dalibar ta hanyar hanata yin jarrabawa saboda tana sanye da hijabi.

 

Wasu Alkalai da Ma’aikatan Kotunan Kano Sun Gamu da Fushin Babbar Jojin Jihar

 

A cewar Yankaji, “Muna Allah-wadai kan abin takaicin da ya faru a jiya Jumu’a, 17 ga watan Afrilun shekarar 2026, a cibiyar jarrabawar Peter Harvard Schools CBT Centre Kubwa ta Abuja, na wulakanta dalibarmu ta hanyar hanata yin jarrabawar UTME saboda tana sanye da hijabi”.

 

Ya kara da cewa wannan lamari ba kawai nuna wariya ba ne, har ma take mata hakki karara na ‘yancin addini da mutuncin ɗan Adam, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

 

Akwai Hannun Mahukunta a Matsalar Tsaron da ke Addabar Arewacin Najeriya Najeriya – Zargin ICHR

 

Haka kuma kungiyar ta ce ta ɗauki wannan lamari a matsayin abin tayar da hankali, rashin adalci, kuma abin ƙyama wanda ke nuna rashin kula da ‘yancin addinin dalibai Musulmi a fadin ƙasar.

 

A ƙarshe sanarwar ta buƙaci a gudanar da zuzzurfan bincike domin fitarwa da dalibar hakkinta, ta yadda hakan zai zama izina da kuma yin kandagarkin faruwar irin haka anan gaba.

 

Kungiyoyi 293 na Jam’iyyar PDP Sun Koma APC a Jihar Yobe

The post MSSN ta yi Allah-wadai da Cin Zarafin Daliba Musulma a Wajen Jarrabawar UTME a Abuja appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow