Masarautar Kano ta Musanta Labarin Sarki Sunusi ya Samu Carry Over a Jami’ar Northwest

Daga Bashir Gasau.   Masarautar Kano ta musanta labarin da ke yawo cewa, Sarki Muhammadu Sanusi II, ya gaza cika sharuddan karatunsa na digirin lauya harma ya samu Carry-Over.   Babban Sakataren Ofishin Sarkin, Muhammad Ado, ne ya musanta labarin da ke yawo a dandalin sada zumunta a jiya Lahadi, wanda ke zargin cewa Sarki Sanusi ya fadi wani […] The post Masarautar Kano ta Musanta Labarin Sarki Sunusi ya Samu Carry Over a Jami’ar Northwest appeared first on GTR .

Masarautar Kano ta Musanta Labarin Sarki Sunusi ya Samu Carry Over a Jami’ar Northwest


















Daga Bashir Gasau.

 

Masarautar Kano ta musanta labarin da ke yawo cewa, Sarki Muhammadu Sanusi II, ya gaza cika sharuddan karatunsa na digirin lauya harma ya samu Carry-Over.

 

Babban Sakataren Ofishin Sarkin, Muhammad Ado, ne ya musanta labarin da ke yawo a dandalin sada zumunta a jiya Lahadi, wanda ke zargin cewa Sarki Sanusi ya fadi wani kwas a cikin darusansa.

 

SIBLING: Abin Koyi ga Kasa Wajen Farfaɗo da Ilimin Aikin Gona ta Hanyar Haɗin Guiwar Gwamnati da Bangarori Masu Zaman Kansu

 

Ya kara da cewa Sarki Sanusi ya yi rajista a matsayin dalibi a shekara ta biyu a tsarin digiri na farko a fannin Shari’ar Musulunci da Dokokin Bai-daya na Jami’ar Northwest da ke Kano, inda ya ce bisa bayanan da suke da su, maki guda daya kacal ne ya rage wa Sarkin don ya kai matakin daraja ta daya (First Class).

 

Sarkin Rano ya Ɗaga Darajar Wasu Dagatai Biyu Zuwa Hakimai

 

A cewar sanarwar, “Mun halarci wani taro da daliban fannin lauya na jami’ar suka shirya a ranar Asabar, kuma wani dalibi ne ya dauki wannan bidiyon, amma maganar ba gaskiya ba ce kuma Sunday Dare bai kasance babban bako mai gabatarwa a wajen taron ba”.

 

Tuni wasu majiyoyi daga Makarantar suka tabbatarwa da Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN), cewa har yanzu ba a fara jarrabawa a makarantar ba, amma ana sa ran farawa a yau Litinin.

 

Gwamnan Bauchi ya Buƙaci Rundunar Sojin Najeriya ta Kafa Sabuwar Bataliya a Yankin Alkaleri

The post Masarautar Kano ta Musanta Labarin Sarki Sunusi ya Samu Carry Over a Jami’ar Northwest appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow