Manoma Kada ku Karaya Domin Yanzu ba Lokacin Daina Noma Bane – Dujiman Gombe

Daga Aliyu Gerengi Gombe.   Shugaban Hadaddiyar Ƙungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN) reshen jihar Gombe, Alhaji Modibbo Sadeeq Ahmad Nafada (Dujiman Gombe), ya shawarci manoman kasar da kada su karaya a sha’anin noma.   Dujiman Gombe, ya baiyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya ce wannan lokaci […] The post Manoma Kada ku Karaya Domin Yanzu ba Lokacin Daina Noma Bane – Dujiman Gombe appeared first on GTR .

Manoma Kada ku Karaya Domin Yanzu ba Lokacin Daina Noma Bane – Dujiman Gombe

Daga Aliyu Gerengi Gombe.

 

Shugaban Hadaddiyar Ƙungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN) reshen jihar Gombe, Alhaji Modibbo Sadeeq Ahmad Nafada (Dujiman Gombe), ya shawarci manoman kasar da kada su karaya a sha’anin noma.

 

Dujiman Gombe, ya baiyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya ce wannan lokaci ba na daina noma bane.

 

Lokaci ya yi da Kanawa za su Farka Kan Matsalar Fadan Dabar da ta Addabe su – Tasi’u Soja

 

A cewarsa, “Mutane da dama sun karaya saboda farashin kayan abinci ya sauka a wannan shekarar, alhali kuma farashin taki, kayan aikin gona da na sufuri na ci-gaba da ƙaruwa. Amma gogaggun manoma sun san cewa harkar noma tana tafiya ne a zagaye-zagaye”.

 

“Farashin da ya yi ƙasa a yau na iya zama ƙarancin abinci a gobe, domin idan manoma da yawa suka rage noma saboda ƙarancin riba a wannan kakar, akwai yiwuwar Najeriya ta fuskanci ƙarancin masara, shinkafa, dawa, gero da sauran hatsi a shekara mai zuwa. Kuma duk lokacin da kayan abinci suka yi ƙaranci, farashinsu yana yin tashin gwauron zabi”. Inji Shugaban AFAN na jihar Gombe.

 

Zan Gyara Kura-kuran Gwamnatocin Baya Idan ‘Yan Kaduna Suka Zaɓe ni – Honarabul Jafaru Sani

 

Adan haka ya ce ya kamata manoma masu hikima su shirya tun yanzu domin cin moriyar kakar dake tafe, ta hanyar noman dukkan hatsin da al’umma ke matuƙar buƙata, ko da kuwa ta hanyar haɗa ƙungiyoyin haɗin guiwa ne domin tallafa wa juna da kuma adana hatsi yadda ya kamata bayan girbi.

 

Bugu da kari ya ce tsaron abinci yana farawa ne daga manomi domin Ƙasar da ba za ta iya ciyar da kanta ba, ba ta samun cikakken ci-gaba, saboda haka akwai buƙatar Manoma musamman Matasa su yi nomansu a daminar bana duk da ƙalubalen da ake fuskanta.

 

A ƙarshe ya ce kada al’umma ta jira sai kasuwanni sun zama babu kayan abinci, sannan za a gane muhimmancin noma.

 

‘Yan Siyasa ne ke Ɗaukar Nauyin ‘Yan Dabar Jihar Kano – AHRCF

The post Manoma Kada ku Karaya Domin Yanzu ba Lokacin Daina Noma Bane – Dujiman Gombe appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow