Majalisar Tsaron Jihar Yobe ta Gargadi Al’umma Kan Rikicin Siyasa

Daga Sani Gazas Damaturu.   Majalisar tsaron jihar Yobe ƙarkashin jagorancin gwamna, Mai Mala Buni, ta gargaɗi al’ummar jihar kan shiga rikicin Siyasa   Da yake magana da manema labarai bayan fitowa daga taron, kwamishinan ‘yan sanda jihar, Usman Kamfani Jibrin, ya ce hukumomin tsaro suna cikin shiri sosai kuma za su magance duk wani […] The post Majalisar Tsaron Jihar Yobe ta Gargadi Al’umma Kan Rikicin Siyasa appeared first on GTR .

Majalisar Tsaron Jihar Yobe ta Gargadi Al’umma Kan Rikicin Siyasa

Daga Sani Gazas Damaturu.

 

Majalisar tsaron jihar Yobe ƙarkashin jagorancin gwamna, Mai Mala Buni, ta gargaɗi al’ummar jihar kan shiga rikicin Siyasa

 

Da yake magana da manema labarai bayan fitowa daga taron, kwamishinan ‘yan sanda jihar, Usman Kamfani Jibrin, ya ce hukumomin tsaro suna cikin shiri sosai kuma za su magance duk wani yunkuri na kawo cikas ga zaman lafiyar jihar, yana mai cewa, duk wani mutum ko wata kungiya da ke da hannu a daukar nauyin ko shiga harkar tada hankalin siyasa ko ta’addanci za su fuskanci fushin doka.

 

UDUTH ya Sami Nasarar Yin Dashen Ƙoda Karo na Biyu, Albarkacin Tunawa da Gudunmawar Sultan Muhammadu Bello a Fannin Kiwon Lafiya

 

Haka kuma ya yaba wa al’ummar jihar kan yadda suka gudanar da aiyukansu cikin kwanciyar hankali a lokacin zaɓen fidda gwani na Majalisar kasa da aka gudanar, inda ya shawarci duk wani mutum ko wata kungiya da bata gamsu da abin da aka yi ba, ta nemi hakkinta bisa doka ta hanyar hukumomin da aka kafa don kula da koken jama’a kan lamarin.

 

A ƙarshe ya shawarci jama’a da su kasance masu lura da dukkan motsin wani bako ko mutane a harkokin su na yau da kullum.

 

Kwankwaso na Yiwa Tinubu Aiki ne a Fakaice Don ya Sake Lashe Zaɓen 2027 – Kakakin Gwamnan Kano

The post Majalisar Tsaron Jihar Yobe ta Gargadi Al’umma Kan Rikicin Siyasa appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow