Lokaci ya yi da Talakawan Najeriya za su Farka – CHRCDI

Daga Bashir Gasau.   Ƙungiyar kare haƙƙin dan adam da bada agaji ta Centre for Human Rights and Charity Development Initiative (CHRCDI), ta baiyana wannan lokaci a matsayin wanda ya kamata talakawa su gane ƙarfinsu.   Da yake zantawa da GTR Hausa, Shugaban gudanarwar Kungiyar, Kwamared Tasi’u Idris Soja, ya ce shekaru da dama al’umma […] The post Lokaci ya yi da Talakawan Najeriya za su Farka – CHRCDI appeared first on GTR .

Lokaci ya yi da Talakawan Najeriya za su Farka – CHRCDI

Daga Bashir Gasau.

 

Ƙungiyar kare haƙƙin dan adam da bada agaji ta Centre for Human Rights and Charity Development Initiative (CHRCDI), ta baiyana wannan lokaci a matsayin wanda ya kamata talakawa su gane ƙarfinsu.

 

Da yake zantawa da GTR Hausa, Shugaban gudanarwar Kungiyar, Kwamared Tasi’u Idris Soja, ya ce shekaru da dama al’umma na fama da wahala, rashin tsaro, talauci da rashin kulawa, duk da suna da ikon canza wannan hali.

 

Kada Mu Bari Bambancin Siyasa ya Jawo Ƙiyayya a Tsakaninmu – Ibraheem Kachallah Macheena

 

A cewar Soja, “Muna kira a gareku da ku tashi tsaye tunda lokacin siyasa yazo, don mu nuna cewa mu ne muke da ƙarfi ba su ba. Ku tuna Ƙuri’arku ita ce makamin ku, adan haka kada ku siyar da ita saboda kuɗi ko son rai”.

 

Duk Wanda ya Haura Shekaru 55 Bazai yi Takara a ADC ba – Nafi’u Bala

 

Ya kara da cewa bai kamata Talakawa su bari a yaudaresu da alkawuran ƙarya ba, ya kamata su zaɓi shugabanni masu gaskiya, tsoron Allah, masu kishin jama’a ba masu amfani da su ba.

 

A ƙarshe ya ce idan al’umma ta yi shuru wahala za ta ci-gaba, amma idan ta tashi canji zai tabbata, adan haka ya yi fatan ‘Yan Najeriya za su tashi su canza ta hanyar zabe, domin gobensu na hannunsu.

 

Yadda Masu Ƙwacen Babur Suka Guntule Min Hannu – Sallaman Sarkin Bakar Sarkin Rano

The post Lokaci ya yi da Talakawan Najeriya za su Farka – CHRCDI appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow