Lokaci ya yi da Kanawa za su Farka Kan Matsalar Fadan Dabar da ta Addabe su – Tasi’u Soja

Daga Bashir Gasau.   Shugaban hukumar gudanarwar kare haƙƙin dan adam ta Najeriya, Kwamared Tasi’u Idris Soja, ya ce lokaci ya yi Kanawa za su Farka kan matsalar Dabar da ta addabe su.   Tasi’u Soja ya baiyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya ce ya zama […] The post Lokaci ya yi da Kanawa za su Farka Kan Matsalar Fadan Dabar da ta Addabe su – Tasi’u Soja appeared first on GTR .

Lokaci ya yi da Kanawa za su Farka Kan Matsalar Fadan Dabar da ta Addabe su – Tasi’u Soja

Daga Bashir Gasau.

 

Shugaban hukumar gudanarwar kare haƙƙin dan adam ta Najeriya, Kwamared Tasi’u Idris Soja, ya ce lokaci ya yi Kanawa za su Farka kan matsalar Dabar da ta addabe su.

 

Tasi’u Soja ya baiyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya ce ya zama wajibi al’ummar Kano su farka daga barcin da suke yi na sakaci akan matsalar daba da ta addabi jihar.

 

A cewarsa, “Wannan matsala ba ta mutum daya bace, ba ta unguwa daya bace, kuma ba ta gwamnati kadai bace. Matsala ce da ta zama tamkar wutar da ke cin rayuwar matasa, lalata iyalai, tare da jefa al’umma cikin tsoro da tashin hankali”.

 

Haɗakar Ƙungiyoyin Fararen Hular Jihar Zamfara Sun Ziyarci CP Ahmad Muhammad

 

“Gaskiya mai ɗaci ita ce, dukkan bangarori suna da kaso a wannan bala’in da ke damun al’ummar jihar Kano”. Inji Tasi’u Soja.

 

Gwamnati tana da alhakin samar da aikin yi, ilimi, da tsaro ga matasa. Idan matashi ya rasa abin yi, ya rasa makoma, ya rasa kulawa, to masu amfani da shi za su same shi cikin sauki.

 

A ɓangaren Iyaye ma suna da nauyi la’akari da yadda wasu suka zubar da tarbiyya, wasu sun kasa bibiyar ‘ya’yansu, wasu kuma suna ganin kudin da yaran ke kawowa ba tare da tambayar inda suke samo su ba.

 

Hukuncin Kisa ta Hanyar Rataya ne ya Dace da Kwankwaso da Ganduje – Abdulkarimu Daiyabu

 

Su kuwa ‘Yan siyasa suna daga cikin manyan masu ruruta wannan matsala a sakamakon yadda a lokacin siyasa suke amfani da matasa a matsayin makami, suna basu kudi, kwaya, da makamai domin tada hankali. Bayan zabe kuma sai su barsu cikin kangin rayuwa da tashin hankali.

 

Jami’an tsaro suma akwai tambayoyi akansu. Me yasa wasu bata-gari suke yawo da makamai amma ba a daukar mataki a Kansu ? Me yasa wasu lokuta ana sakin wadanda aka kama saboda wani mai fada aji ya shiga?

 

Dadin dadawa masu kudi da wasu ‘yan kasuwa ma suna da hannu. Wasu suna ɗaukar ‘yan daba domin kare kasuwancinsu ko anfani da su wajen tsoratar da mutane. Hakan yana kara karfafa wannan annoba.

 

Sanata Wadada ya Samu Tikitin Takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a Jam’iyyar APC

 

Daga ɓangaren Malamai kuma suna da rawar takawa sosai, domin ya zama wajibi su kara fadakarwa akan illar daba, Shan kwaya, da tashin hankali a Mumbari da makarantunsu waɗanda suka zama wuraren gyaran tarbiyya da ceto matasa.

 

Adan haka ya yi kira da kakkausan murya ga gwamnatin Kano da ta dauki mataki na gaskiya, ba wai na daukar hoto ba kawai. A hukunta masu daukar nauyin daba komai girman su. A samar wa matasa aiki, horaswa, da tallafi. A hada hannu tsakanin gwamnati, malamai, iyaye, da jami’an tsaro domin ceto makomar jihar.

 

A ƙarshe ya ce idan ba a tashi tsaye yanzu ba, gobarar daba zata ci gaba da cin rayukan matasa da lalata martabar jihar Kano.

 

Bidiyo: Gwamnan Zamfara ya Tarbi Tawagar Sojojin da Aka Kawo Don Fatattakar ‘Yan Ta’adda

The post Lokaci ya yi da Kanawa za su Farka Kan Matsalar Fadan Dabar da ta Addabe su – Tasi’u Soja appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow