Kwankwaso na Yiwa Tinubu Aiki ne a Fakaice Don ya Sake Lashe Zaɓen 2027 – Kakakin Gwamnan Kano

Daga Bashir Gasau.   Gwamnatin Kano ta ce da amincewar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya koma wajen Tinubu a jam’iyyar APC.   Kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya baiyana hakan a yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce da amincewar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, […] The post Kwankwaso na Yiwa Tinubu Aiki ne a Fakaice Don ya Sake Lashe Zaɓen 2027 – Kakakin Gwamnan Kano appeared first on GTR .

Kwankwaso na Yiwa Tinubu Aiki ne a Fakaice Don ya Sake Lashe Zaɓen 2027 – Kakakin Gwamnan Kano

Daga Bashir Gasau.

 

Gwamnatin Kano ta ce da amincewar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya koma wajen Tinubu a jam’iyyar APC.

 

Kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya baiyana hakan a yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce da amincewar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Gwamnan ya tuntubi Shugaba Tinubu kan batun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

 

Hotuna: Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta Baiyana Nasarar da ta Samu a Cikin Kwanaki 30

 

A cewar Sunusi Bature, “Batun sauya shekar na daga cikin tattaunawar siyasa da ake yi a bayan fage gabanin babban zaɓen shekarar 2027, kuma Kwankwaso da tsohon Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, suna sane da shirin kuma suna goyon bayansa”.

 

A ƙarshe ya zargi Sanata Rabi’u Musa da yi wa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, aiki a fakaice domin taimaka masa wajen sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2027.

 

Na fi Kowa Cancantar Zama Gwamnan Jihar Katsina – Tsohon Shugaban DSS na Najeriya Lawal Daura

The post Kwankwaso na Yiwa Tinubu Aiki ne a Fakaice Don ya Sake Lashe Zaɓen 2027 – Kakakin Gwamnan Kano appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow