Kungiyar CAN ta Bukaci Gwamnatin Najeriya ta Sanya Dokar ta Baci a Sha’anin Tsaron Kasar

Daga Kallamu Galadima Dambo.   Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), ta buƙaci gwamnatin tarayya ta sanya dokar ta baci a sha’anin tsaron kasar.   Shugaban kungiyar na arewacin Najeriya, Rabaram Joseph Hayap, ne ya baiyana hakan a yayin zantawar sa da GTR Hausa a Abuja, inda ya ce akwai matuƙar damuwa da takaici kan halin […] The post Kungiyar CAN ta Bukaci Gwamnatin Najeriya ta Sanya Dokar ta Baci a Sha’anin Tsaron Kasar appeared first on GTR .

Kungiyar CAN ta Bukaci Gwamnatin Najeriya ta Sanya Dokar ta Baci a Sha’anin Tsaron Kasar

Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), ta buƙaci gwamnatin tarayya ta sanya dokar ta baci a sha’anin tsaron kasar.

 

Shugaban kungiyar na arewacin Najeriya, Rabaram Joseph Hayap, ne ya baiyana hakan a yayin zantawar sa da GTR Hausa a Abuja, inda ya ce akwai matuƙar damuwa da takaici kan halin da tsaron kasar ke ciki.

 

Ƙungiyar Equity Alliance ta Kai Karar ADC ga EFCC da ICPC Kan Zargin Tafka Maguɗi a Zaɓen Fidda Gwani a Kaduna

 

Ya kara da cewa har yanzu matsalar tsaron kasar karuwa take yi maimakon ta ragu, duba da yadda ake yi wa al’ummar kasar ɗauki ɗai-ɗai, kuma a dukkan sassan kasar.

 

Adan haka ya ce akwai buƙatar shugabannin kasar a dukkan matakai musamman gwamnatin tarayya, da su ɗauki dukkan matakan da za su zama sun kare rayuka da dukiyoyin al’umma Najeriya.

 

Ƙarashen Zantawar GTR Hausa da Ministan Tsaron Najeriya, Christopher Gwabin Musa

 

A hannu guda ya ce yanzu haka kungiyar ta umarci Kiristocin kasar da su gudanar da Azumi da Addu’oi, daga ranar 12 zuwa 14 ga watan Yunin da muke ciki, da nufin neman daukin Ubangiji akan matsalar tsaron.

 

A ƙarshe kungiyar ta buƙaci sauran addinai da su gudanar da Addu’oi na musamman, domin a hada hannu wajen komawa ga Allah, ko ya kawo sauki akan matsalar tsaron ta inda ba a zata ba.

 

Gigin Tsufa ne ya Sanya Babachir Lawal Yin Munanan Kalamai Akan Atiku Abubakar – Na’omi Abel

The post Kungiyar CAN ta Bukaci Gwamnatin Najeriya ta Sanya Dokar ta Baci a Sha’anin Tsaron Kasar appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow