Kare ya Ciji Mutane 18 a Ƙaramar Hukumar Garko ta Kano

Daga Bashir Gasau.   Hukumar Tsaron Gandun Daji ta Najeriya reshen jihar Kano, ta tabbatar da hallaka wani Kare da ya Ciji Mutane 18, bayan ya haukace a Ƙaramar Hukumar Garko.   Kakakin Hukumar na jihar Kano, CSF Usman Abdullahi Umar, ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR […] The post Kare ya Ciji Mutane 18 a Ƙaramar Hukumar Garko ta Kano appeared first on GTR .

Kare ya Ciji Mutane 18 a Ƙaramar Hukumar Garko ta Kano












Daga Bashir Gasau.

 

Hukumar Tsaron Gandun Daji ta Najeriya reshen jihar Kano, ta tabbatar da hallaka wani Kare da ya Ciji Mutane 18, bayan ya haukace a Ƙaramar Hukumar Garko.

 

Kakakin Hukumar na jihar Kano, CSF Usman Abdullahi Umar, ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya ce akalla mutane 11 Mahaukacin Karen ya Ciza a cikin garin Garko, baya ga Mutane 7 a garuruwan Raba, Kadage, Gurjiya da kuma Dausai.

 

A cewar Usman, “Iftila’in ya faru ne da misalin Karfe 2 na ranar Laraba, 24 ga watan Satumbar shekarar 2026, inda al’ummar Ƙaramar Hukumar suka kai rahoton faruwar lamarin ga Ofishinmu na yankin wanda ke ƙarkashin kulawar Auwalu Muhammad”.

 

Haka kuma ya ce a halin yanzu Jami’ansu sun bazama neman karin Karnuka guda Biyu da ake zargin sun kamu, domin ganin suma an hallaka su.

 

A karshe ya shawarci al’ummar Ƙaramar Hukumar ta Garko da su kara sanya idanu akan dukkan wani Kare da suka gani, domin ɗaukar matakin yin kandagarkin faruwar wannan lamari.

 

 

The post Kare ya Ciji Mutane 18 a Ƙaramar Hukumar Garko ta Kano appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow