Jihar Neja ta Sami Gagarumin Ci-gaba a Sha’anin Noma da Kiwo Cikin Shekarun Ukun Gwamna Bago – Kwamishina Rabe

Daga Kallamu Galadima Dambo.   Kwamishinan Ma’aikatar kula da Noma da Kiwo ta jihar Neja, Honarabul Umar Ahmed Rabe, ya baiyana shekaru Ukun Gwamnatinsu ƙarkashin jagorancin, Muhammad Umar Bago, a matsayin wadda ta shafe ta sauran Gwamnonin jihar da suka gabata.   Umar Rabe, ya baiyana hakan ne a yayin zantawarsa da GTR Hausa, inda […] The post Jihar Neja ta Sami Gagarumin Ci-gaba a Sha’anin Noma da Kiwo Cikin Shekarun Ukun Gwamna Bago – Kwamishina Rabe appeared first on GTR .

Jihar Neja ta Sami Gagarumin Ci-gaba a Sha’anin Noma da Kiwo Cikin Shekarun Ukun Gwamna Bago – Kwamishina Rabe

Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

Kwamishinan Ma’aikatar kula da Noma da Kiwo ta jihar Neja, Honarabul Umar Ahmed Rabe, ya baiyana shekaru Ukun Gwamnatinsu ƙarkashin jagorancin, Muhammad Umar Bago, a matsayin wadda ta shafe ta sauran Gwamnonin jihar da suka gabata.

 

Umar Rabe, ya baiyana hakan ne a yayin zantawarsa da GTR Hausa, inda ya ce dalilinsa na fadin haka shine saboda irin nasarorin da suka samu a fannin Noma da Kiwo a waɗannan shekaru.

 

Gwamnatin Neja da Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sun Rage Matsalar Tsaro da Kaso me Yawa – VGN

 

A cewar Rabe, “Gwamnan Neja me ci ne ya fara budewa manomanmu Ido a fannin noman zamani, lamarin da har ma’aikatan gwamnati suka gane cewa akwai arziki me tarin yawa”.

 

A hannu guda ya baiyana yadda bayan zuwan gwamnatinsu a shekarar 2023 suka gano gwamnati bata da kididdigar Makiyayan jihar da dabbobinsu, wanda hakan ne zai basu damar sanin matsalolinsu domin a magance musu.

 

Albashin Naira Milyan Ɗaya ne ya Dace da Ma’aikatan Najeriya ba Dubu 100 ba – NLC

 

Adan haka ma’aikatarsa ta tattara bayanan Makiyayan da ke jihar, domin samar musu da tsarikan da za su inganta rayuwarsu da dabbobinsu, saboda suma su shiga sahun masu amfanar mulkin dimokuraɗiyya.

 

A ƙarƙashin tsarin an tallafa wa wadanda suke neman agaji da kuma waɗanda suka gamu da wani Iftila’i na haddura ko kuma matsalar tsaro, wadanda suke zaune waje daya harma da Makiyaya masu yawo.

 

Budaddiyar Wasika ga Al’ummar Jihar Kano – Ambasada Mukhtar Gashash

 

Bugu da kari ya ce sun samar musu da ababen more rayuwa ciki harda Famfo me amfani da hasken rana (Solar Borehole) sama da guda Sittin, wanda ya basu damar samun tsaftataccen ruwan da zasu sha tare da dabbobinsu.

 

Dadin dadawa ya ce an samar da Kwamitocin da za su kare hakkokin Makiyaya da Manoma, tare da sulhunta dukkan wani rikici da ya taso a tsakanin bangarorin biyu, matakin da ya magance kashi 70 na matsalolin da ake yawan samu a tsakaninsu.

 

Jam’iyyar ADC Tsagin Nafiu Bala ta Tabbatar da Chris Uba a Matsayin Dan Takararta na Shugaban Kasa

 

A ƙarshe ya ce ma’aikatarsa ta samar da guraben aiyukan yi fiye da kowacce ma’aikata a jihar Neja, a sakamakon yadda aikin hukumar ke da alaka da fannoni daban-daban na rayuwar al’ummar jihar.

 

‘Yan Fashin da Ake Zargin Sun Addabi Kasuwar Daji Sun Shiga Hannun ‘Yan Sandan Zamfara

The post Jihar Neja ta Sami Gagarumin Ci-gaba a Sha’anin Noma da Kiwo Cikin Shekarun Ukun Gwamna Bago – Kwamishina Rabe appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow