IHRC ta Nuna Fargaba Kan Yawaitar Ficewar Makiyaya da Dabbobinsu Daga Najeriya

Daga Bashir Gasau.   Kungiyar kare haƙƙin dan adam ta International Human Rights Commission (IHRC-RFT Nigeria), ta bayyana matuƙar damuwarta kan yadda dubban makiyaya tare da Milyoyin dabbobinsu ke ci-gaba da barin ƙasar zuwa maƙwabtan ƙasashe domin neman wuraren kiwo, ruwa, tsaro da zaman lafiya.   Shugaban Ƙungiyar na Najeriya, Kaftin Abdullahi Bakoji Adamu me […] The post IHRC ta Nuna Fargaba Kan Yawaitar Ficewar Makiyaya da Dabbobinsu Daga Najeriya appeared first on GTR .

IHRC ta Nuna Fargaba Kan Yawaitar Ficewar Makiyaya da Dabbobinsu Daga Najeriya












Daga Bashir Gasau.

 

Kungiyar kare haƙƙin dan adam ta International Human Rights Commission (IHRC-RFT Nigeria), ta bayyana matuƙar damuwarta kan yadda dubban makiyaya tare da Milyoyin dabbobinsu ke ci-gaba da barin ƙasar zuwa maƙwabtan ƙasashe domin neman wuraren kiwo, ruwa, tsaro da zaman lafiya.

 

Shugaban Ƙungiyar na Najeriya, Kaftin Abdullahi Bakoji Adamu me ritaya, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa makiyaya daga sassa daban-daban na ƙasar ba da son ransu suke barin Najeriya ba.

 

Hotuna: Yadda Aka Daura Auren Ma’aikacin Premier Radio Kano, Ibrahim Hassan Hausawa

 

A cewarsa, “Sun danganta hakan da rashin wadatattun wuraren kiwo da burtalai, matsalolin tsaro, hare-haren ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane, satar dabbobi, tsangwama daga wasu hukumomi da al’ummomi”.

 

Bugu da kari Kungiyar ta kuma nuna damuwa kan yadda ake yi wa al’ummar Fulani kudin goro, a matsayin masu aikata laifi saboda aiyukan wasu kaɗan daga cikin masu laifi.

 

Hukumar Tace Fina-finai ta Kano ta Rufe Shagon Siyar da Magungunan Gargajiya na Kausar Unique Empire Ltd

 

“Al’ummar Fulani na daga cikin manyan al’ummomin Najeriya masu Milyoyin jama’a, kuma suna daga cikin waɗanda suka fi shan wahala a hannun ‘yan ta’adda ta hanyar kashe su, sace su, kwace musu dabbobi da lalata hanyoyin rayuwarsu, Saboda haka ɗora wa al’umma baki ɗaya laifin wasu tsirarun mutane ba adalci ba ne, kuma yana ƙara haifar da wariya, rashin fahimtar juna da rarrabuwar kawuna a cikin al’umma”. Inji Shi.

 

Adan haka ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da su ɗauki matakan gaggawa domin inganta tsaro, kare haƙƙin kowane ɗan ƙasa ba tare da nuna bambanci ba, dawo da hanyoyin kiwo da wuraren kiwo da doka ta tanadar wa makiyaya tun shekaru aru-aru, da ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai tsakanin al’ummomi.

 

Bata-gari ne ke Amfani da Rigar Fulani Wajen Bata Mana Suna – Baba Othman Ngelzarma

 

Bugu da kari ta ja hankali kan cewa ci-gaba da wannan hijira na iya yin illa ga tattalin arzikin ƙasa, musamman a fannin kiwo, samar da Nama da Madara, da kuma wadatar abinci.

 

A ƙarshe sanarwar ta ce zata ci-gaba da aiki tare da gwamnati, al’ummomi da sauran masu ruwa da tsaki wajen kare haƙƙin bil’adama, inganta zaman lafiya da samar da mafita mai ɗorewa ga matsalolin da ke shafar makiyaya da sauran ‘yan Najeriya.

 

Alamomi Gane Balagar Yara da Matakan da Iyaye ya Kamata su Ɗauka – Malama Juwairiyya

The post IHRC ta Nuna Fargaba Kan Yawaitar Ficewar Makiyaya da Dabbobinsu Daga Najeriya appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow