IHRC ta Buƙaci Gwamnatin Kano ta Gaggauta Magance Matsalar Tsadar Kayan Aikin Jinya a Asibitocin Gwamnati

Daga Bashir Gasau.   Ƙungiyar kare haƙƙin dan adam ta International Human Rights Commission – Relief Fund Trust (IHRC-RFT), ta yaba da Ƙoƙarin Gwamnatin Jihar Kano tare da kira da ta gaggauta magance matsalar tsadar kayan aikin Jinya a Asibitocin Gwamnati.   Daraktan kungiyar na Najeriya, Kaftin Abdullahi Bakoji Adamu (Rtd), ne ya baiyana hakan […] The post IHRC ta Buƙaci Gwamnatin Kano ta Gaggauta Magance Matsalar Tsadar Kayan Aikin Jinya a Asibitocin Gwamnati appeared first on GTR .

IHRC ta Buƙaci Gwamnatin Kano ta Gaggauta Magance Matsalar Tsadar Kayan Aikin Jinya a Asibitocin Gwamnati












Daga Bashir Gasau.

 

Ƙungiyar kare haƙƙin dan adam ta International Human Rights Commission – Relief Fund Trust (IHRC-RFT), ta yaba da Ƙoƙarin Gwamnatin Jihar Kano tare da kira da ta gaggauta magance matsalar tsadar kayan aikin Jinya a Asibitocin Gwamnati.

 

Daraktan kungiyar na Najeriya, Kaftin Abdullahi Bakoji Adamu (Rtd), ne ya baiyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya ce suna samun ƙorafe-ƙorafe da dama daga jama’a, musamman kan irin nauyin kuɗaɗen da marasa lafiya ke fuskanta a wasu asibitocin gwamnati.

 

Wajibin Dan Najeriya ne ya Fito ya Kawar da Mulkin Zalunci na Jam’iyyar APC – Honarabul Philip Anthony

 

A cewar Bakoji, “Muna jinjinawa Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusif, a bisa jajircewarsa da ƙoƙarin gwamnatinsa wajen inganta rayuwa da jin daɗin al’ummar Jihar, harma da shirye-shirye da sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa a fannoni daban-daban na ci-gaban jihar”.

 

Toh sai dai kuma duk da wannan yabo, ƙungiyar ta ce ya zama wajibi ta jawo hankalin Gwamnan kan ƙorafe-ƙorafen da al’umma ke ci-gaba dayi, dangane da tsadar wasu kayan aikin jinya a wasu asibitocin gwamnati da ke jihar.

 

Shugaba Tinubu ya Umarci ICPC ta Binciki Hukumar Bogi ta PFIPC

 

“Mun yi imanin cewa lafiya ita ce ginshiƙin rayuwa da walwalar al’umma, saboda haka tabbatar da samun ingantacciya kuma cikin sauki ya kamata ya kasance a sahun farko na manyan abubuwan da gwamnati ke bai wa fifiko”.

 

Harma sanarwar ta ce daya daga cikin Asibitin da ta karbi ƙorafe-ƙorafen shine “Imam Wali” da ke unguwar Janbulo, wanda ake karɓar kusan Naira 4,000 domin gwajin wanda zai ba da jini (blood donor screening), Naira 2,000 kan ledar jini (blood bag), da kuma Naira 300 kan canular.

 

Hotuna: Yadda CP Omolori ya Ziyarci Garin Azare Kan Rikicin da ya Faru a Tsakanin Kungiyoyin Matasa

 

A dai-dai lokacin da ake samun irin waɗannan kayayyaki a wasu kantunan sayar da magunguna (chemist) a farashi mafi sauƙi, inda ledar jini akan Naira 1,700, yayin da canular kan Naira 150. Kuma akwai wasu kayayyaki da dama da ake zargin ana siyar da su da tsada fiye da yadda ake samu a kasuwa.

 

Mafari kenan da IHRC ta ce hakan na haifar da tambayoyi masu muhimmanci game da arha da sauƙin samun kulawar lafiya, wanda hakan zai yi wahala talakawa su fahimci dalilin da zai sa kayan aikin jinya su fi tsada a asibitin gwamnati fiye da cibiyoyin lafiya na masu zaman kansu.

 

An Kuma Hukunta Wasu Alkalai da Ma’aikatan Kotunan Jihar Kano Saboda Aikata Laifuka Daban-daban

 

Adan haka kungiyar ta roki Gwamnan Kano da ya binciki wannan lamari cikin gaggawa domin babu wata walwala da ta fi muhimmanci fiye da ta lafiya, tare da ɗaukar matakan da za su rage wa al’umma wannan nauyi don ƙara inganta amincewar jama’a a tsarin kiwon lafiyar jihar.

 

A karshe sanarwar ta bukaci Ma’aikatar Lafiya da shugabannin asibitocin gwamnati na jihar da su binciki waɗannan ƙorafe-ƙorafe, ta hanyar sake duba tsarin farashin kayan aikin jinya, tare da tabbatar da cewa suna kasancewa masu sauƙin samu, masu arha, kuma cikin gaskiya da adalci ga dukkan al’umma.

 

Muna da Yakinin Al’ummar Zaria za su Bamu Damar Wakiltarsu Tunda Sun Gani a Kasa – Aliyu Lawal Cairo

The post IHRC ta Buƙaci Gwamnatin Kano ta Gaggauta Magance Matsalar Tsadar Kayan Aikin Jinya a Asibitocin Gwamnati appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow