Hukumar Shari’a ta Kano ta Jagoranci Bude Masallacin Jumu’a na Shaikh Tijjani Usman Zangon Bare-bari, da ke Kurna Titin Shinge

Daga Bashir Gasau.   Hukumar Shari’a ta jihar Kano, ta Jagoranci bude Masallacin Jumu’a na Shaikh Tijjani Usman Zangon Bare-bari, da ke Kurna Titin Shinge a ƙaramar hukumar Dala.     Mamba a Kwamitin gudanarwar hukumar, Imam Ibrahim Inuwa, ne ya jagoranci Sallar Jumu’ar bayan ya gabatar da Hudubar ta yau, 29 ga watan Mayun […] The post Hukumar Shari’a ta Kano ta Jagoranci Bude Masallacin Jumu’a na Shaikh Tijjani Usman Zangon Bare-bari, da ke Kurna Titin Shinge appeared first on GTR .

Hukumar Shari’a ta Kano ta Jagoranci Bude Masallacin Jumu’a na Shaikh Tijjani Usman Zangon Bare-bari, da ke Kurna Titin Shinge

Daga Bashir Gasau.

Hukumar Shari’a ta jihar Kano, ta Jagoranci bude Masallacin Jumu’a na Shaikh Tijjani Usman Zangon Bare-bari, da ke Kurna Titin Shinge a ƙaramar hukumar Dala.

Hukumar Shari’a ta Kano ta Jagoranci Bude Masallacin Jumu'a na Shaikh Tijjani Usman Zangon Bare-bari, da ke Kurna Titin Shinge

Mamba a Kwamitin gudanarwar hukumar, Imam Ibrahim Inuwa, ne ya jagoranci Sallar Jumu’ar bayan ya gabatar da Hudubar ta yau, 29 ga watan Mayun shekarar 2026.

Da yake jawabi bayan bude Masallacin, Imam Ibrahim Inuwa, wanda ya kasance Limamin Masallacin Ja’en, ya ce ya zama wajibi al’ummar yankin su godewa Ubangiji a bisa Ni’imar da yayi musu na samun wannan Masallaci me girman gaske.

Hukumar Shari’a ta Kano ta Jagoranci Bude Masallacin Jumu'a na Shaikh Tijjani Usman Zangon Bare-bari, da ke Kurna Titin Shinge

Adan haka ya hore su da su kasance masu raya masallacin ta hanyar gudanar da Sallah, karatuttukan littattafai Musulunci da sauran aiyukan da suka shafi addini.

Shaikh Muhammad Abu Musa, shine Daraktan kula da sashen Wa’azi da bude Masallatai harma da Musuluntar da Maguzawa na hukumar, ya buƙaci ‘Yan Kwamitin Masallacin da su yi dukkan mai yiwuwa, wajen samar masa da abubuwan da yake bukata ta fuskar kula da kuma kayan amfanin yau da kullum.

Hukumar Shari’a ta Kano ta Jagoranci Bude Masallacin Jumu'a na Shaikh Tijjani Usman Zangon Bare-bari, da ke Kurna Titin Shinge

Daga bisani Shugaban Kwamitin Masallacin, Alhaji Musa Yahaya Mumini, ya ce yanzu haka shirye-shiryensu yayi nisa wajen samar da abubuwan da za su amfani al’ummar yankin kamar wajen wankan Gawa, Motar ɗaukar marasa lafiya, makarantar koyar da yara da matan Aure, ta hanyar amfani da kuɗaɗen Shagunan da suka kasance mallakar Masallacin.

A ƙarshe al’ummar yankin sun sha alwashin yin dukkan mai yiwuwa wajen bada tasu gudunmawar, domin raya wannan masallaci ta yadda zai zama wata babbar cibiyar yada addinin Musulunci a fadin ƙaramar hukumar ta Dala dama jihar Kano gaba-ɗaya.

Hukumar Shari’a ta Kano ta Jagoranci Bude Masallacin Jumu'a na Shaikh Tijjani Usman Zangon Bare-bari, da ke Kurna Titin Shinge

The post Hukumar Shari’a ta Kano ta Jagoranci Bude Masallacin Jumu’a na Shaikh Tijjani Usman Zangon Bare-bari, da ke Kurna Titin Shinge appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow